Gasar Kofin Duniya da labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 20 zuwa 26, Yuli, 2026

Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran Gasar Kofin Duniya da aka kammala da kuma sauran labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 20 zuwa 26 ga watan Yuli, 2026.

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Otamendi ya yi ritaya daga bugawa Argentina wasa

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan wasan baya na Argentina Nicolás Otamendi ya sanar da yin ritayarsa daga bugawa ƙasarsa wasa yana da shekara 38.

    Wannan ce gasar kofin duniya ta huɗu da ya halarta inda ya shiga a canji a wasan da Spain ta doke su 1-0 ta kuma ɗauki kofi a ranar Lahadi.

    "Yau na tsinci kaina cikin rubuta kalmomi mafiya wuya a rayuwata ta kwallon kafa," kamar yadda ya rubuta a Instagram.

    "Ina ban kwana da tawagar ƙasata Argentina, amma dai ina cikin farin cikin wakiltar ƙasata."

  2. An sa ranar sauraren ƙarar da Senegal ta ɗaukaka kan Afcon

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun sauraren kararrakin wasanni ta sanya ranar sauraren karar da Senegal ta daukaka kan kwace mata kofin Afcon da ta ci na 2025.

    CAF ce ta sauya hukuncin ta ayyana Morocco a matsayin wadda ta lashe gasar da aka kammala a January, wadda Senegal ta ci 1-0.

    'Yan wasan Senegal ne suka fice daga filin saboda an bai wa Morocco fenariti a karshen wasa, lokacin ana fafatawa babu ci.

    Bayan bata lokacin da aka yi na mintina 17, yan wasan Senegal din sun dawo cikin fili, kuma Brahim Diaz ya zubar da fenaritin da aka ba su.

    A ranar 25 ga watan Maris Senegal ta daukaka karar a gaban kotun, tana neman a yi watsi da hukuncin Caf a dawo mata da kofinta.

    Hukuncin Caf ya ayyana Morocco ta yi nasara kan senegal da ci 3-0.

    Kotun ta sa 8 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta saurari ƙarar da Senegal ta ɗaukaka.

  3. Kane na tattaunawa da Bayern Munich kan sabon kwantaragi

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Harry Kane na tattaunawa da Bayern Munich kan sabon kwantaragi da gwarzuwar gasar Jamus ɗin.

    Kwantaragin kyaftin ɗin Ingilan za ta ƙare ne a ƙarshen sabuwar kakar da za a shiga. sai dai Bayern na son ɗan wasan ya ci gaba da zama a ƙungiyar.

    Shi ma Kane yana sane da cewa ƙungiyar na son ya tsawaita kwantaraginsa, saboda ana tsammanin hakan ya zama ya kammalu nan da makonni masu zuwa.

    Kane ya koma Bayern ne daga Tottenham a 2023 a wani ciniki da ya kai fan miliyan 86.

    Dan wasan kuma ya ji dadin nasarorin da ya samu tare da Munich, inda ya taimakawa ƙungiyar ta lashe Bundesliga guda biyu da kuma German Cup ɗaya.

    Kyaftin din ya ciwa ƙasarsa kwallo shida a gasar Kofin Duniya, ya kuma ci wa Munich kwallo 146 a wasa 134 da ya buga mata tun lokacin da ya koma ƙungiyar.

    Barcelona dai tana ta bibiyar dan wasan yayin da ƙungoyoyin Saudiyya ke neman ɗaukarsa da kwantaraginsa ya ƙare.

  4. Za a yiwa Rodri tiyata a gadon bayansa

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Sabon kocin Manchester City Enzo Maresca ya ce za a yi wa Rodri tiyata a bayansa ranar Juma'a.

    Dan wasan tsakiyar mai shekara 30 ya taka rawa wajen taimakawa kasarsa ta lashe kofin duniya a karshen makon jiya, kuma shi ne ya lashe kyautar dan wasan da ya fi kowa kokari.

    Amma kaka biyu da ya buga a baya a kungiyarsa ya yi ta fama da jiya ne - amma wani rauni da ya ji a kokon gwiwarsa ya hana shi sakat, ya sa bai taka rawar gani ba a kakar 2024-25.

    Kyaftin din Sifaniyan wanda ya taba lashe Ballo d'Or ya dawo kan ganinyarsa ne a wannan gasar ta Kofin Duniya.

    A tattaunawarsa da manema labarai ta farko sabon kocin na City ya ce dan wasan na bukatar a yi masa tiyata a ranar Litinin.

  5. Belgium ta naɗa Mark van Bommel sabon kocinta

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Belgium ta naɗa tsohon dan wasan Netherlands Mark van Bommel a matsayin sabon kocinta zuwa 2028.

    Kyaftin ɗin Belgium ɗin mai shekara 49 ya gaji Rudi Garcia, wanda ya bar tawagar bayan cire Belgium a wasan kusa da dab da na ƙarshe bayan Sifaniya ta doke ta.

    An amince Mark van Bommel zai karɓi aikin ne a hukumance daga ranar 15 ga watan Agusta mai zuwa.

    A bayan nan Van Bommel yana kocin ƙungiyar Royal Antwerp ne, kuma su ne suka cin kofin gasar Belgium kuma shi ne ya lashe Belgian Super Cup bayan shekaru biyu da ya kwashe yana aiki da kungiyar

    "Babbar girmamawa ce zama kocin tawagar Belgium," in ji Van Bommel. "Belgium na da 'yan wasa masu kyau da za su iya zama wasu a gobe. Ni da tawagata ta koci za mu gina tawagar da za ta zama ta kai ga nasara, kwarewa da kuma babban buri ya isa hujjar gogayya da duk wata tawaga."

  6. Arsenal ta shirya biyan £70m kan Bruno Guimaraes

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal ta shirya biyan fan miliyan 70 kan ɗan wasan tsakiya kuma kyaftin ɗin Newcastle Bruno Guimaraes.

    Dan wasan Brazil ɗin shi ne babban wanda Arsenal ta sa a gaba, shi ma kuma ɗan wasan yana son komawa gwarzuwar gasar Premier.

    Ko ƙungiyarsa Newcastle ta san ɗan wasan na da fatan komawa buga wasa Gunners.

    Ana ci gaba da tattaunawa tsakanin ƙungiyoyin biyu kuma rahotanni na cewa za a gaggauta cinikin ne cikin kwanakin da suka rage a fara gasar Premier.

    Sai dai duka cinikin ya dogara ne kan ƙoƙarin Arsenal na iya biyan kuɗin da Newcastle ke buƙata.

    Arsenal na yunkurin neman yadda za ta ƙara ƙarfafa tsakiyarta domin mamaye gasar da ta lashe a bara.

  7. Dan wasan da ake zargi da shan hodar iblis bayan gudun wuce iyaka

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana zargin ɗan wasan Australia da ya buga mata kofin duniya Cristian Volpato da ta'ammali da hodar iblis bayan kama shi yana gudun wuce iyaka a mota.

    'Yan sanda ne suka tsayar da shi har sau biyu a birnin Sydney lokacin da yake gudun wuce iyakar, duka bai tsaya ba a daren.

    An tsayar da matashin dan wasan mai shekara 22 a wata mota ƙirar BMW a kan gadar Anzac da misalin ƙarfe 11:05 na yamma a ranar Alhamis, bayan an ganshi yana gudu tsakanin kilomita 86 zuwa 94 a awa daya, kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.

    An dakatar da shi a gefen titi domin yi masa gwaji daga baya aka ga yana ta'ammali da hodar.

    An ƙara kama shi yana gudun kilomita 109 cikin awa guda.

    'Yan sandan New South Wale sun sa masa dokar hana gudu, tare da kwace lasisin tuƙinsa har na tsawon wata shida, wanda hakan ke nufin ba zai yi tuƙi ba a yankin nan da lokacin da aka ɗiba masa.

  8. Pep Guardiola ya yi watsi da tayin zama kocin Italiya.

    Guardiola

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon Kocin Manchester City Pep Guardiola ya yi watsi da tayin da asar italiya ta yi masa ma zama koci tawagar wallon ƙafar ƙasar.

    A farkon wannan makon ne shugaban Hukumar Kwallon Kafar Italiya (FIGC), Giovanni Malago, ya bayyana cewa sun tattaunawa da Guardiola game da batun.

    A ranar Alhamis, babban daraktan hukumar, Paolo Maldini, ya ce mutum na farko da Italiya ta fara tuntuɓa shi ne tsohon ɗan wasanta Carlo Ancelotti, wanda a yanzu shi ne kocin tawagar ƙasar Brazil.

    Sai dai Ancelotti ya amince da ci gaba da aikinsa a Brazil, lamarin da ya sa suka mayar da hankali kan Guardiola.

    TGo sai dai shi ma ya ƙi amincewa da karɓar aikin, yana mai cewa har yanzu yana son ƙarin hutu domin samun damar ci gaba da kasancewa da iyalansa, da yin tafiye-tafiye.

    A ƙarshen kakar da ta gabata ne Guardiola ya bar Manchester City bayan shafe kusan shekara 10 a ƙungiyar.

  9. Jamus ta naɗa Jurgen Klopp sabon kocin ƙasar

    Jurgen Klopp

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙwallon ƙafar Jamus ta bayyana tsohon kocin Liverpool, Jurgen Klopp, a matsayin sabon kocin tawagar ƙasar.

    Naɗin nasa na zuwa kwanaki bayan murabus ɗin Julian Nagelsmann, wanda ya ajiye aiki bayan da tawagar Jamus ta fice daga Gasar Kofin Duniya tun a matakin ƴan 32.

    Klopp, wanda ke cikin manajojin a duniyar ƙwallon ƙafa - bai riƙe wani aikin horaswa ba tun bayan da ya bar Liverpool shekaru biyu da suka gabata.

    Aikinsa na baya-bayan nan shi ne shugaban harkokin ƙwallon ƙafa na duniya na kamfanin Red Bull, tare da yin sharhi a talabijin kan harkokin ƙwallon kafa.

    Yanzu yana fuskantar ƙalubalen farfaɗo da martabar wannan babbar tawagar Turai, wadda ta taɓa lashe Kofin Duniya har sau huɗu a tarihinta.

  10. Arsenal ta ɗauki dan wasan Girka Tzolis £34m

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal ta ɗauki wani kwararren dan wasan gaban ƙasar Girka Christos Tzolis daga Club Brugge kan fan £34m.

    Mai shekara 24 ya koma kungiyar da ta lashe Premier ne a abin da suka kira dogon kwantaragi.

    Tzolis ya ci kwallo 43 a da bada 45 aka ci a wasa 108 da ya buga wa Clib Brugge.

    Ya koma Arsenal ne saboda tafiyar Leadro Trossard zuwa Besiktas a farkon wannan watan.

    Arsenal za ta so kare kambunta da ta ci bayan shekara 22 rabonta da shi.

  11. Norway na shirin ɗaukaka ƙara kan jan katin Balogun

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kwallon ƙafa ta Norway na duba yiwuwar shigar da ƙara gaban kwamtin Fifa kan hukuncin janyewa dan wasan Amurka Folarin Balogun jan katin da aka ba shi a gasar kofin duniya.

    Kamata ya yi ɗan wasan na Amurka ba zai buga wasan zagaye na 'yan 16 da ba da suka fafata da Belgium saboda katin da aka ba shi a wasan da suka doke Bosnia da ci 2-0.

    Amma bayan shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya sa baki sai aka janye hukuncin dakatarwar da aka yi masa zuwa nan da wata 12.

    Fifa ba ta bayar da wani dalili ba bayan ambato wata doka a kundinta da ta yarda a dakatar da hukunci kan ɗan wasa.

    Daga baya Balogun ya buga wasan, kuma Belgium ta casa su da ci 4-1.

    Cikin wata sanarwa da Hukumar NFF ta turawa BBC, shugaban Hukumar Lise Klaveness ya ce "za su dauki hukunci mai tsauri kan hakan" ba za su kyale ba.

    Dama tun a baya NFF ɗin ta shigar da ƙara kan kyautar zaman lafiya ta Peace Prize da aka bai wa Trump tana ƙalubalantar rashin cancantarsa.

  12. Saliba hutu ya ke buƙata ba tiyata ba - rahotanni

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni na cewa mahukunta Faransa da Arsenal sun cimma yarjejeniyar ba za a yi wa dan wasansu da ke buga baya aiki ba, saboda raunin da yake fama da shi.

    Maimakon haka rahotannin sun ce 'hutu yake buƙata ba tiyata ba a bayansa'.

    Saliba wanda ɗaya ne daga cikin jigo a tawagar Faransa da aka yi wa tsammanin taka rawar gani a kofin duniya amma Spain ta cinye ta a wasan kusa da na ƙarshe, kuma ta yi rashin nasara a hannun Ingila a neman na uku, ya buga wa ƙasarsa wasanni 7 a gasar.

    Jigo ne shi a tawagar Arsenal da ta lashe gasar Premier a kakar da ta gaba, kuma ta je wasan ƙarshe a gasar Zakarun Nahiyar Turai ta Champions Lig.

    Wasu masana dai na ganin yawan jinyar da matasan 'yan kwallo ke fama da ita, na da alaƙa da yawan wasannin da suke bugawa ƙungiyoyi da kasashensu, ba kuma sa samun cikakken hutun da ya kamata.

  13. Villa ta karɓi Garnacho a matsayin aro daga Chelsea

    /

    Asalin hoton, Getty Images

    Aston Villa ta amince da yarjejeniyar aro kan ɗan wasan gefe na Chelsea Alejandro Garnacho zuwa ƙarshen kakar 2026/27 tare da zaɓin saya.

    Dan wasan mai shekara 22 ya kammala gwajin lafiyarsa a Birmingham a wani mataki na yarjejeniyar shekara huɗu idan Villa ta amince ta saye shi daga baya.

    Ba dai a bayyana sharadin da sai an cika ba za a sayi ɗan wasan, amma za a bayyana ta ne da zarar an cika sharudan, kamar dai yawan wasannin da ɗan wasan na Argentina zai buga a kaka mai zuwa.

    Chelsea ta yi amannar sharuɗan ba su da wuyar cikawa dan haka a ƙarshe za ta samu abin da take fata na darajar ɗan wasan da ta kai fan miliyan 43.

    Barin Chelsea da ɗan wasan ya yi ya biyo bayan ɗan kar Morgan Rogers da aka yi kan kuɗi fan miliyan 117 a ranar Talata.

  14. Guardiola na dab da zama kocin Italy

    a

    Asalin hoton, PA Media

    Shugaban Hukumar Kwallon ƙafa ta Italiya Giovanni Malago ya ce sun tattauna da Pep Guadiola domin zama sabon kocin Italiya na gaba.

    Pep da ya bayar Manchester City bayan kwashe shekaru 10 masu cike da nasara a Ingila, wanda cikinsu ya lashe Premier shida da FA uku da Kofin Lig biyar da kuma ChampionsLig ɗaya.

    Italiya ba ta da kocin tun bayan da Gennaro Gattuso ya yi murabus a watan Afrilu saboda gaza samun tikitin gasar Kofin Duniya sama da sau ɗaya a jere.

    Tun da fari Sky Italiya ce ta fara rawaito cewa wani abu na shirion faruwa tsakanin kocin mai shekara 55 da kuma Hukumar Kwallon Ƙafa ta Italiya FIGC.

    A wata tattaunawa da ya yi da wata kafar labaran wasanni Malago ya tabbatar da alaƙar yana cewa "maganar kuɗi ce kawai ta yi saura tsakaninsu da Pep".

    Hukumar kwallon ƙafa ta Italiya ta aike da wakilai da suka haɗa da mai koyar da dabarun wasannin ƙasar wanda tsohon dan wasanta ne Paolo Maldini da mai bashi shawara Leonardo sun je har Barcelona sun tattauna da Guardiola na tsawon kwanaki uku.

  15. Newcastle ta amince ta biya £34m kan ɗan wasan Manaco Bamba

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    ƙungiyar kwallon kafa ta Newcastle ta amince da cinikin da ya kai £34m kan dan wasan tsakiya na Manaco Aladji Bamba.

    Dan wasan na Faransa mai shekara 20 wanda ya fara bugawa ƙasar wasa a watan Agustan 2025, ya kamata ya isa Tyneside a ranar Alhamis ɗin yau domin yi masa gwajin lafiya ya kuma sanya hannu kan kwantaraginsa.

    Newcastle ta sayar da Sandro Tonali ga Tottenham a watan jiya kuma ta shiga kasuwa domin samun wani matashin dan wasan ta dauka a karo na biyu, bayan ɗaukar Sean Steur dan shekara 18 daga Chelsea.

    Wani wanda take shirin ɗauka shi ne Johan Manzambi daga Freigurg wanda ya zaɓi ya koma Aston Villa a makon jiya.

  16. Ana binciken Inter Miami kan karya doka a cinikin Casemiro

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar shirya gasar Major Lig Soccer ta Amurka ta ce tana bincike kan zargin karya dokar da ƙungiyar Inter Miami ta yi wajen ɗaukar dan wasan tsakiya na Brazil Casemiro.

    A ranar Laraba ne Miami ta sanar da ɗaukar ɗan wasan mai shekara 34 da ya bar Manchester United a ƙarshen kakar nan.

    Ya koma ƙungiyar ne bisa yarjejeniyar shekara guda amma akwai zaɓin tsawaita ta zuwa watan Yunin 2029.

    Ba jimawa sai Hukumar MLS ta fitar da sanarwar tana 'duba zargin da ake na take doka a cinikin' kuma ana dora laifin ne kan ƙungiyar.

    "Inter Miami na tara duk wasu bayanan da suka kamata masu alaƙa da cinikin domin kare kanta," a cewarsu.

    Za a yi binciken ne kan damar da kungiyoyi ke da ita na ɗaukar ɗan wasa idan yana son ya je gasar.

    Kazalika ƙungiyoyin gasar na da damar sanyi buƙatar daukar 'yan wasa biyar a lokacin guda, kuma za su iya cire wanda suke so ko su ƙara wanda suke so.

  17. Ina son Mac Allister da Alisson su ci gaba da zama a Liverpool- Iraola

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Liverpool Andoni Araola na son ɗan wasan tsakiya Alexis Mac Allister da mai tsaron ragar ƙungiyar Alisson su ci gaba da zama a ƙungiyar.

    Dan wasan Argentina Mac Allister na da shekaru biyu da suka rage masa a ƙungiyar cikin shekaru biyar da ya sanya wa hannu lokacin da yazo a 2023.

    Dan shekara 27 har yanzu bai fara magana kan sabunta kwantaraginsa ba, wanda hakan ya janyo jita-jita kan cewa zai bar Andfield a wannan kakar.

    Iraola ya shaida wa manema labarai a Chicago cewa yana son fara wasannin share kaka a Amurka da waɗannan 'yan wasan nasa.

    "Ina ganin Alexis na daya daga cikin 'yan wasa masu kyau na ƙungiyar nan cikin tsawon shekaru, kuma ya taka rawar gani a kofin duniya, dan haka ba wani abu ba ne wasu ƙungiyoyin su nemi manyan 'yan wasanmu," in ji kocin.

    "Hakan na faruwa a kasuwar saye da sayerwar 'yan wasa.Kuma ni ina son ci gaba da aiki da yan wasana masu kyau. Kuma nan gaba zan ɗauki sabbin 'yan wasa."

    Alisson na da shekara ɗaya da ta rage masa masa a Anfield kuma tuni Juventus ta nuna muradinta a kansa, Amma Araola a shirye yake ci gaba da aiki da golan mai shekara 33 a ƙungiyar.

  18. Ina ganin ba sai an hukunta Leandro Paredes ba - Gavi

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan wasan tsakiya na Spain Gavi ya ce shi bai amince a dakatar da dan wasan Argetina ba Leandro Paredes saboda fito na fiton da ya yi a filin wasa ba, bayan kammala wasan ƙarshe na Gasar Duniya.

    Yan wasan Aregentina Parades da Molina da Almada da kuma mai taimakawa koci Roberto Ayala duka an gansu da hannu cikin rikicin lokacin da Spain ke murnar kammala gasar da ta ci 1-0.

    An ga Parades ya shaƙi wuyan Eric ɗan wasan Spain da kuma kayar da Gavi yana yunkurin taushe shi yayin da shi ma Almada ya taimaka masa.

    Parades bayan ya kayar da ɗan wasan na Barcelona ya nemi ya dake shi a fuska.

    Tuni Fifa ta kafa kwamitin bincike kan lamarin, tare da alƙawarin tara mai tsoka kan duk wanda aka kama da laifi.

    "Ban ga wani abun ɓacin rai ba, ba sai an dakatar da shi ba (Parades), kamar yadda Gavi ya shaida wa jaridar El Partidazo de COPE.

  19. Sabbin fuskokin masu horarwar da za a gani a Nahiyar Turai

    Bayan kammala gasar Kofin Duniya da aka yi a Amurka da Mexico da kuma Canada, rashin nasarar da wasu ƙasashe suka yi na neman zama sanadin kawo sauye-sauye a tawagoginsu.

    'Yan wasa da dama sun ajiye takalmansu kazalika masu horaswa. Amma wannan maƙalar za ta yi duba kan wasu ƙasashe da ke neman kawo sauyi a fannin horarwarsu.

    Faransa:

    Tun gabanin rashin nasarar da ta yi a kofin duniya ake yaɗa jita-jitan cewa za a sauya mai horarsa da tawagarta.

    An ta cewa tsohon kocinta Zinedine Zidane zai maye gurbin kocinta na yanzu Didier Deschamp.

    Amma bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Spain managa ta ƙara ƙarfi, manyan jaridu turai ciki har da Fabrizio Romano sun rawaito cewa Zidane zai jagoranci Faransa har zuwa June 2030.

    Wannan na nufin zai jagoranci ƙasar zuwa manyan gasar da suka haɗa da Nations League 2027 Euros 2028 da kuma Kofin duniya 2030.

    Zidane ya yi wasa da Deschamp a 1998, tawagar da suka ci kofin duniya bayan doke Brazil 3-0.

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Jurgen Klopp:

    Bai zo da mamaki ba jin cewa Jurgen Klopp zai zama kocin Jamus na gaba ba, saboda daɗewa da ya yi ba tare da wata ƙungiya da yake jagoranta ba.

    Babban abin da ya tabbatar da burinsa na jan ragamar Jamus shi ne tattaunawar da aka yi tsakanin Hukumar kwallon Kafa ta Jamus da tsohon kocin tawagar Julian Negelsman ya ce sun cimma matsaya da hukumar kan ajiye aikinsa.

    Hukumar ta tabbatar da cewa Jurgen Klopp zai jagoranci Jamus sai dai ba a bayyana tsayin lokacin ba da kuma lokacin da zai fara aiki.

    Tun daga 2014 da Jamus ta ci Kofin Duniya a hannun Argentina, Jamus ba ta ƙara cin wasa ba a mataki na sili daya kwale.

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Pep Guardiola:

    Aikin gaban Pep Guardiola zai zama babba ne, domin zai farfaɗo da tawagar da ake ganin ta zama mushen gizaga.

    Hukumar kwallon ƙafa ta ITaliya ta aike da wakilai da suka haɗa da mai koyar da dabarun wasannin ƙasar wanda tsohon dan wasanta ne Paolo Maldini da mai bashi shawara Leonardo sun je har Barcelona sun tattauna da Guardiola na tsawon kwanaki uku.

    Pep wanda ya yi nasara a zamansa a spain lokacin da ya jagoranci Barcelona da zamansa a Jamus inda ya yi kocin Beyern Munich sai kuma inda da ya horas da Manchester City, watakila Itali ta zama inda zai yi kocin na gaba.

    Zai iya zama koci na biyu dan wata ƙasar da zai jagoranci Italiya kuma na farko tun shekarun1960.

    Tsofaffin 'yan wasan ƙasar irinsu Roberto Mancini da Andrea Pirlo suma sun nuna shaawarsu kan aikin.

    Guardiola mai shekara 55, aikin ba zai bashi wuya ba saboda yana jin yaren Italiya sosai, lokacin da ya zauna a ƙasar tsakanin shekarar 2001 zuwa 2003.

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Mark van Bommel:

    Mark van Bommel tsohon dan wasan Barcelona kuma ɗan asalin Netherland rahotanni na cewa zai karbi aikin horas da Belgium na tsawon shekara biyu zuwa watan Yunin 2028.

    Belgium ma kamar sauran ƙasashen da suka fuskanci koma baya a gasar kofin Duniya ta kai matakin wasan kusa da dab da naƙarshe a gasar inda gwarzuwar gasar Spain ta doke ta da ci biyu da ɗaya.

    Rudi Garcia wanda tsohon dan wasan Faransa ne shi ne ya kai Belgium kofin duniya, kuma ya kabi aikin ne a 2025.

    Ana sa ran Van Bommel zai jagoranci tawagar zuwa shekarar 2028, bayan gasar Euro.

    a

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Nijar da Mali da Burkina Faso na son karɓar baƙuncin Afcon

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun miƙa takardar haɗaka ta neman karɓar baƙuncin gasar ƙwallon ƙafa ta Afirka, Afcon a shekarar 2032.

    Jami'an ƙasashen sun gabatar da takardar buƙatar ne ga shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF), Patrice Motsepe.

    Shugabannin hukumomin kula da ƙwallon ƙafa na ƙasashen sun gana da Motsepe a birnin New York na Amurka a ranar Asabar, tare da Kanar Djibrilla Hima Hamidou, wakili a hukumar ƙwalllon ƙafa ta duniya FIFA, kuma ɗaya daga cikin manyan hukumar ƙwallon ƙafa ta Jamhuriyar Nijar.

    A ranar Talata ne hukumar ƙwallon ƙafa ta Mali (FEMAFOOT) ta sanar da ganawar da aka yi, inda ta ce za a yi amfani da gasar wajen bunƙasa "haɗin kai tsakanin ƙasashen yankin da kuma haɓɓaka ƙwallon ƙafa a Afirka."

    Miƙa takardar neman karɓar baƙuncin ta biyo bayan nuna sha'awar hakan da ƙasashen AES suka yi.

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Mali ta ce za ta yi aiki tare da sauran ƙasashen biyu wajen yin "ingantaccen shirin karɓar gasar" wanda zai kawo sabon ci gaba a harkar ƙwallon ƙafa a nahiyar.

    Har yanzu hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka ba ta riga ta zaɓi ƙasar da za ta karɓi baƙuncin gasar ta 2032 ba, gasar da ake yi duk bayan shekara biyu, tana tattara zaƙaƙuran masu taka leda na nahiyar.

    A shekarun baya-bayan nan ne ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Faso suka kafa ƙungiyar ƙasashen yankin Sahel ta AES bayan ficewa daga ƙungiyar haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (Ecowas), bayan jerin juyin mulki a ƙasashen.

    AES ta ce manufarta ita ce bunƙasa haɗn kai tsakanin ƙasashen uku, musamman a ɓangaren tsaro da kasuwanci da kuma tattalin arziƙi.