Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 17/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 17/11/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Trump na ganawa da shugabannin duniya a Philippines.

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya gana da shugabannin Australia, da Indiya da Japan a farkon ziyarar da yake yi a nahiyar Asiya, wadda ake sa ran za ta ƙare da ganawarsa da shugabannin China da Rasha a ranar Alhamis.

    A yayin ziyarar tasa a Philippines, Trump ya kuma rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta farko kan kasuwanci da Thailand, inda ya ce yarjejeniyar za ta cire dukkan harajin da ake ɗora wa kayayyakin da Amurka ke fitarwa zuwa ƙasar.

    Shugaban Amurkan zai tattauna batutuwan tsaron yankin, da kasuwanci da fasaha a wasu ƙarin ganawa a rana ta ƙarshe ta taron shugabannin yankin da ke gudana a Manila, kafin ya wuce China.

  2. Tsohon shugaban kamfanin Nvidia ya ce a shirye yake ya koma kan mukaminsa

    Tsohon babban jami’in gudanarwa na kamfanin Nvidia, Jensen Huang, ya ce a shirye yake ya amince da kiran da ake yi masa na komawa kan mukaminsa, idan har kwamitin gudanarwar kamfanin ya yanke shawarar dawo da shi.

    Huang ya bayyana hakan ne a karon farko tun bayan da ya yi murabus a makon da ya gabata, sakamakon bayyanar zargin cewa ya yi hulɗar soyayya da wata mata da ake zargi da yi wa China leƙen asiri.

    Ya zuwa yanzu, sama da mutane dubu 190 ne suka sanya hannu kan wata takardar koke da ke neman a dawo da shi kan mukaminsa.

    A halin da ake ciki, Nvidia na shirin kafa wani kwamiti na musamman da zai riƙa sa ido kan batutuwan tsaron ƙasa da kuma dokokin fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.

  3. Shugabar kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya ta gargaɗi kotunan zaɓe kan rashawa

    Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Najeriya, Monica Dongban-Mensem, ta gargaɗi sakatarori da ma'aikatan kotunan sauraron ƙararrakin zaɓe da su guji karɓar cin hanci ko yin duk wani abu da zai kawo cikas ga gudanar da shari'a gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

    Ta yi gargaɗin cewa duk wani ma'aikaci da aka samu da hannu a harkokin cin hanci da rashawa zai fuskanci hukunci, tana mai jaddada cewa wannan aiki kira ne na yi wa ƙasa hidima, ba wata dama ba ce ta tara dukiya ko amfana da kai.

    Dongban-Mensem ta yi wannan gargaɗi ne a ranar Litinin, yayin buɗe wani taron horaswa na tsawon kwanaki biyu da aka gudanar a Abuja, mai taken: “Sabbin Hanyoyin Gudanar da Ayyukan Rajista Domin Inganta Gudanar da Kotunan Sauraron Ƙararrakin Zaɓe.”

    Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce an shirya taron ne domin shirya ma'aikatan kotunan sauraron ƙararrakin zaɓe da ƙwarewar gudanarwa da ake buƙata wajen kula da shari'o'in da suka shafi zaɓe, musamman yayin da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa ke gabatowa, wanda aka tsara gudanarwa a ranar 16 ga Janairu, 2027.

  4. Trump na son ganawa da Kim Jong Un

    Shugaban Amurka Donald Trump na halartar taron ƙungiyar ƙasashen ASEAN a Philippines, kafin ya zarce zuwa taron APEC da za a gudanar a China.

    Haka kuma ya bayyana burinsa na ganawa da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un.

    Rahotanni na nuna cewa akwai yiwuwar shugabannin su haɗu a karon farko tun bayan da Trump ya koma kan karagar mulkin Amurka a Fadar White House.

    Ana sa ran Trump zai gana da Shugaban ƙasar China Xi Jinping da kuma Shugaban Rasha Vladimir Putin.

  5. An kashe wata mata tare da jikkata mutum 10 a Yammacin Kogin Jordan

    Kafofin yaɗa labaran Falasɗinu sun ce wata mata Bafalasɗiya ta mutu yayin da wasu mutum 10 suka jikkata sakamakon harbe-harbe da ake zargin Yahudawa ƴan kama wuri zauna ne suka yi a wani ƙauye da ke yammacin Jericho, a yankin Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye.

    Jami'an lafiya sun ce matar mai shekaru 60 ta rasu ne bayan harsashi ya same ta a ka.

    Lamarin ya faru ne a wata unguwa da Yahudawa 'yan kama wuri zauna suka karɓe iko da ita a farkon wannan wata.

    Sojojin Isra'ila sun ce harbe-harben sun biyo bayan wani hari da wata motar Falasɗinawa ta yi inda ta kutsa wa motar Isra'ila.

  6. Bincike ya cewa kisan Jeffrey Epstein aka yi a gidan yari

    Wani ƙwararren a fannin binciken ƙwayar halittar ɗan'adam daga Amurka ya shaida wa BBC cewa binciken da ya yi kan hotunan gawar marigayi Jeffrey Epstein ya nuna cewa an kashe shi a gidan yari.

    Farfesa Michael Freeman, ya ce bayan nazarin takardun rahoton binciken gawar da jami'in binciken ya yi, ya yi imanin cewa an shake wuyan Epstein ne, mai yiwuwa ta baya.

    An tsinci gawar Epstein, wanda aka samu da laifukan cin zarafin yara ta hanyar lalata, a gidan yarin da aka ajiye shi da ke New York a shekarar 2019, yayin da yake jiran fara shari'a kan zarge-zargen safarar mata da yara domin yin lalata da su.

    Sai dai jami'ar da ta gudanar da binciken gawar a lokacin ta ce raunukan da aka samu a jikinsa sun yi daidai da mutuwar da ke nuna cewa an rataye shi ne. break

  7. Muna ɗaukar barazanar Iran da matuƙar muhimmanci - Trump

    Donald Trump ya ce yana ɗaukar barazanar da muhimmanci sosai bayan wani rahoton CNN da ya yi magana kan yiwuwar Iran ta kai hari a birnin Washington.

    Shugaban Amurka, wanda ke ƙasar Philippines domin halartar taron ASEAN, ya ce yayin da yake amsa tambayar wani ɗan jarida: "Ina fatan hakan ba zai faru ba, amma muna ɗaukar wannan batu da matuƙar muhimmanci."

    Ya kuma ƙara da cewa: "Wannan ne dalilin da ya sa bai kamata su mallaki makamin nukiliya ba."

    Trump ya jaddada cewa yana ɗaukar lamarin da muhimmanci saboda, a cewarsa, "da alama suna da hatsari kuma ba a iya hasashen abin da za su yi."

    Ya yi barazanar cewa idan aka kai irin wannan hari, "za su fuskanci hukunci irin wanda babu wata ƙasa da ta taɓa fuskanta a tarihi."

    Tun da fari, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya yi watsi da rahoton CNN da ya ce Iran na iya shirya tayar da abin da ake kira "dirty bomb" a Washington, yana mai bayyana rahoton a matsayin "zarge-zarge marasa tushe."

  8. Trump ya isa Philippines a ziyarar ƙasashen Asiya

    Shugaban Amurka Donald Trump ya isa Manila domin halartar taron ƙungiyar ASEAN.

    Ana kuma sa ran Shugaban na Amurka zai tashi daga Philippines zuwa China domin halartar taron APEC, inda ake sa ran zai shiga wani taron shugabanni uku da ba a saba gani ba tare da shugaban China Xi Jinping da shugaban Rasha Vladimir Putin a ranar Alhamis.

    Ziyarar tasa zuwa Manila ta zo ne a ranar ƙarshe ta taron shekara-shekara na shugabannin ƙasashen ƙungiyar ASEAN, inda ake sa ran Mista Trump zai halarci tarurruka kan harkokin tsaron yankin da kuma kasuwanci.

    Harajin kwastam da Mista Trump ya ƙaƙaba, da kuma yaƙin da ake yi da Iran, sun haifar da manyan ƙalubale ga Philippines.

    Wannan ita ce tafiyar farko ta Mista Trump zuwa ƙasashen waje tun bayan da Jam’iyyar Republican ta sha babban kaye a zaɓukan tsakiyar wa'adin mulkinsa.

  9. Bahrain ta ce ta kakkaɓo hare-haren Iran a ƙasar

    Gidan talabijin na gwamnatin Bahrain ya ce dakarun ƙasar sun daƙile hare-haren da Iran ta kai, kuma an hana su cimma manufofinsu.

    Tun da farko, rundunar IRGC ta ce ta kai hari kan wata na'urar radar ta dakarun Amurka da ke sansanin Sheikh Isa da ke tsibirin Bahrain.

    Rundunar ta bayyana cewa harin wani ɓangare ne na matakan da take dauka a matsayin martani ga abin da ta kira ayyukan adawa da Amurka ke yi a yankin.

    Sai dai hukumomin Bahrain sun ce an kakkaɓe harin, yayin da har yanzu CENTCOM ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan iƙirarin da Iran ta yi ba.

  10. Mun kai hari kan na'urorin radar Amurka a Bahrain - Iran

    Rundunar kare juyin juya halin Iran (IRGC) ta ce ta kai hari kan na'urar radar ta rundunar sojin Amurka da ke sansanin Sheikh Issa a ƙasar Bahrain.

    A cikin wata sanarwa da sashen hulɗa da jama'a na rundunar ya fitar, ta ce an kai harin ne a matsayin martani ga abin da ta bayyana a matsayin ayyukan adawa da Amurka ke gudanarwa a yankin.

    Kwanaki kaɗan da suka gabata, rundunar IRGC ta ikirarin cewa na'urorinta sun gano tare da sa ido kan dakarun Amurka da ke Bahrain, amma a lokacin rundunar CENTCOM ta Amurka ta musanta iƙirarin.

    Har yanzu CENTCOM ba ta fitar da wata sanarwa ba kan ikirarin kai harin da IRGC ta yi ba.

  11. 'Za mu buɗe mashigar Hormuz ne kawai idan Amurka ta cika sharuɗɗa bakwai'

    Mai magana da yawun sojojin Iran ya ce ba za a sake buɗe mashigar Hormuz ba har sai Amurka ta amince da sharuɗɗa bakwai da Iran ta gindaya.

    Ya kuma gargaɗi jiragen ruwa da su guji amfani da hanyoyin da ya ce Amurka na bayyana a matsayin amintattu.

    Da yake magana a birnin Bandar Abbas, Amir Akraminia ya ce rundunonin sojin Iran suna cikin cikakken shiri, kuma sun karɓe iko da muhimman wurare da ke gabashi da yammacin mashigar Hormuz.

    Ya ƙara da cewa ba za a sake buɗe wannan muhimmiyar hanyar ruwa ba har sai Amurka ta amince da bukatun Iran.

    A cewarsa, jiragen ruwa da ke amfani da hanyoyin da Iran ba ta amince da su ba na iya fuskantar haɗarin nakiyoyin da aka dasa a ƙarƙashin tekun da kuma harbe-harbe.

    Ya ce tsaron jiragen ruwa zai samu ne kawai idan aka haɗa kai da dakarun Iran tare da bin hanyoyin da rundunar soji da kuma rundunar juyin juya halin Iran suka tanada.

    Mai magana da yawun ya kuma yi gargaɗin yiwuwar sake ɓarkewar rikicin soja, yana mai cewa idan aka sake ɗaukar wani mataki da ya kira kuskure, ko kuma ƙasashen yankin suka bi buƙatun Washington da ya bayyana a matsayin haramtattu, sansanonin da muradun abokan gaba za su fuskanci martani cikin gaggawa da karfi.

  12. 'Zan tsaya takarar shugaban ƙasa idan mahaifina ya sauka'

    Babban kwamandan rundunar tsaron ƙasar Uganda (UPDF), Janar Muhoozi Kainerugaba, ya ce zai tsaya takarar shugaban ƙasar idan mahaifinsa, Shugaba Yoweri Museveni, ya sauka daga mulki.

    Ya ce babu wanda zai iya hana shi cimma wannan buri nasa.

    A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata, Muhoozi ya ce yana dogaro ne ga Allah da kuma al'ummar Uganda.

    "Zan tsaya takarar shugaban kasa idan Mzee ya sauka daga mulki. Babu wanda zai hana ni wannan buri. Na ɗora buri ga Allah da kuma ƴan uwana ƴan Uganda," in ji shi.

    Wannan furuci na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan jam'iyyar gwamnati ta National Resistance Movement (NRM) ta musanta rahotannin da ke cewa kwamitinta na ƙoli ya yi watsi da wani kuduri na goyon bayan Muhoozi ya gaji mahaifinsa.

    Sakataren Janar na jam'iyyar NRM, Richard Todwong, ya ce rahotannin da ke ikirarin an gudanar da wani taron sirri na kwamitin a ranar 10 ga Nuwamba ba su da tushe.

    Ya ƙara da cewa jam'iyyar za ta sanar da matsayarta a lokacin da ya dace, ta hanyar hanyoyinta na hukuma.

    Kalaman Muhoozi sun kuma sake tayar da tambayoyi game da yiwuwar sauyin shugabanci a cikin jam'iyyar NRM mai mulki, a daidai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce kan rawar da yake takawa a siyasar kasar.

    Sai dai har yanzu ba a tabbatar ko zai samu isasshen goyon baya a cikin jam'iyyar da zai tabbatar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa ba.

  13. Ba za mu bari yaƙinmu da Iran ya kai shekara biyu ba - Vance

    Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya ce gwamnatin Amurka ba za ta bari yaƙin da take yi da Iran ya ɗauki tsawon shekara biyu ba.

    Ya kuma jaddada cewa shirin nukiliyar Iran na ci gaba da zama barazana ga Amurka.

    "Mun yi wa al'ummar Amurka alƙawarin cewa ba za mu sake shiga yaƙe-yaƙen da ba su da iyaka ba," in ji Vance a wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai ta Fox News ranar Litinin.

    "Haƙiƙa shugaban ƙasa ya yi imanin cewa dole ne a lalata shirin nukiliyar Iran, kuma gaskiya ne cewa wannan shiri barazana ne ga Amurka. Amma ba za mu bari wannan rikici ya rikiɗe ya zama yaƙin da zai ɗauki shekara 10 ko 15 ba, ko ma shekara biyu," in ji shi.

    Kalaman Vance na nuni ne ga shekaru biyun da suka rage wa wa'adin mulki na biyu na Trump.

  14. Iran ta ce ta kama jirgin Amurka maras matuƙi

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta ce dakarunta sun yi kutse cikin tsarin sarrafa jirgin yaƙin Amurka maras matuƙi, ƙirar MQM-10, sannan suka saukar da shi tare da ƙwace shi.

    A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar da safiyar Talata, ta ce an "karbe ikon jirgin ne a sararin samaniyar kudancin tsibirin Qeshm, kafin daga bisani a saukar da shi lafiya".

    IRGC ta ce ta yi hakan ne yayin wani samamen yaƙi ta hanyar na'urorin laturoni (electronic warfare) da ƙwararrun rundunar sojin saman IRGC suka gudanar cikin kwarewa da nasara.

    Har yanzu rundunar sojin Amukra da ke Gabas ta Tsakiya (CENTCOM) ba ta mayar da martani kan ikirarin Iran ɗin ba.

  15. An kai munanan hare-hare Ukraine cikin dare

    Magajin garin Kyiv, Vitaliy Klitschko, ya ce wasu makamai masu linzami da aka harba sun afka wa gadoji biyu da ke kan kogin Dnipro a babban birnin Ukraine.

    Jami'an birnin sun kuma bayyana cewa harin ya shafi layin dogo na ƙarƙashin ƙasa , lamarin da ya sa aka dakatar da zirga-zirga a wani ɓangare na layin na ɗan lokaci.

    Wakilin BBC da ke Kyiv ya ce ya ji ƙarar fashewar wasu abubuwa da daddare, yayin da aka ba da rahoton wani sabon jerin hare-hare da sanyin safiyar yau.

    Rundunar sojin saman Ukraine ta ce an harba makamai masu linzami masu sarrafa kansu zuwa Kyiv daga cikin yankin Rasha.

    Wakiliyar BBC ta ce a wani labarin kuma, shugaban da Rasha ta naɗa a yankin Crimea da take iko da shi ya ce Ukraine ta sake kai hari kan gadar Kerch, wadda ke haɗa yankin da Rasha, a dare na biyu a jere.

  16. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin bayyana mana ra'ayoyinku kan labaran da muke wallafawa