Waɗanda suka tsira daga wani mummunan hari da ƴanbindiga suka kai a jihar Neja sun shaida wa BBC yadda ƴan bindiga suka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu masu yawa a wasu hare-hare da suka kai a lokaci guda kan yankuna huɗu.
Ƴan bindigar, waɗanda aka ce suna sanye da kayan sojoji, sun kai hare-hare kan ƙauyukan Dekara, Gidan Zana, Sabon Gida da Masaka.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya shaida wa BBC cewa an kashe fiye da mutum 40. Sai dai hukumomi sun ce har yanzu ba a tabbatar da haƙiƙanin adadin waɗanda aka kashe ko aka sace ba.
Mazauna yankin na fargabar cewa mutanen da aka yi garkuwa da su na iya zarta adadin da hukumomi suka bayyana.
Wani matashi daga yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya shaida wa BBC cewa mai yiwuwa mutanen da ƴan bindigar suka yi garkuwa da su za su kai kusan 500.
Wannan ƙiyasin ya biyo bayan yaɗuwar wani bidiyo da wata ƴan bindiga suka saki, wanda ya nuna gomman mutane, mata, yara da maza zaune a wani daji.
Matashin ya ce ya gane wasu mutane daga cikin ƴan garinsu a cikin bidiyon.
“Na iya gane mutane da dama. Akwai wani dattijo a cikin bidiyon wanda yake kamar kakana ne. Yana zaune a ƙauyen Gidan Zana,” in ji shi.
Ya ce iyalan mutanen da suka gane ƴan uwansu a cikin bidiyon sun ji daɗin sanin cewa har yanzu suna raye.
Matashin ya ce an binne kusan mutum 30 ranar Litinin, kuma har yanzu ƴan bindigar ba su tuntuɓi mutanen yankin domin neman wani abu na fansar mutanen ba.
Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa mazauna yankuna da dama sun bar gidajensu, inda suka nemi mafaka a wasu jihohin Najeriya da kuma ƙetare iyaka zuwa ƙasar Benin. Wasu daga cikin waɗanda suka tsira kuma na samun kulawa a asibitoci, ciki har da waɗanda suka samu munanan raunuka.
Wani jami’in tsaro ya kuma shaida wa BBC cewa maharan sun dasa bama-bamai a kan hanyoyi, yayin da suke rakiyar mutanen da suka yi garkuwa da su zuwa daji, inda wani yaro matashi ya mutu bayan bam ya tashi da shi yayin da yake ƙoƙarin tserewa.