Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Litinin 5 ga watan Oktoban 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. Yemen ta ƙaddamar da hari don ƙwato Sana'a daga hannun Houthi

    Dakarun gwamnatin Yemen sun ce sun fara ƙaddamar da gagarumin farmaki kan babban birnin ƙasar, Sanaa, da nufin ƙwato birnin daga hannun ƙungiyar Houthi da Iran ke marawa baya.

    Wani gidan talabijin mai alaƙa da Houthi ya ruwaito cewa Saudiyya ta kai hari kan Sanaa.

    Hakan na zuwa ne bayan gamayyar ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta ta kai hare-hare kan ɗaruruwan wurare , a wani yunƙuri na dakile mayaƙan Houthi daga ci gaba da nausawa wasu yankunan.

    Jami'an Yemen sun ce dakarunsu sun ƙwace wasu muhimman wurare a mashigar Bab el-Mandeb, bayan sun fatattaki mayaƙan Houthi daga wannan muhimmiyar mashigar ruwa da ke tekun Maliya.

  2. An kashe aƙalla mutum 28 duk da dokar hana fita a Filato

    An kashe aƙalla mutum 28 a sabbin hare-haren da aka kai a ƙananan hukumomi uku na jihar Filato, duk da dokar hana fita da gwamnatin jihar ta ƙaƙaba a ranar 21 ga Satumba domin dawo da zaman lafiya da hana ci gaba da asarar rayuka.

    Yankunan da abin ya shafa ciki har da Mangu, Bokkos da Barkin Ladi, sun fuskanci hare-hare akai-akai a 'yan makonnin nan.

    Lamarin ya jefa dubban mazauna cikin fargaba, ya kuma kawo cikas ga ayyukan noma da kiwo, tare da tilasta wa mutane da dama barin harkokin samun abincinsu.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a sabon harin da aka kai jiya, an kashe mutum biyu tare da jikkata wasu shida bayan an kai hari kan makiyaya da ke cikin motar ɗaukar kaya a kusa da wani gidan mai da ke Bukuru, a ƙaramar hukumar Jos South ta jihar Filato.

    Harin ya faru ne ƙasa da makonni biyu bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari kan makiyaya a kusa da garin Kassa da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi, inda suka kashe mutum biyar tare da jikkata mutum ɗaya.

    Shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a Jos, ya ce 'yan bindigar sun kai wa motar hari ne da misalin ƙarfe 5:30 yayin da mutanen ke dawowa daga kasuwar shanu zuwa ƙaramar hukumar Bassa.

    Shugaban ya yi allah-wadai da harin, tare da kira ga jami'an tsaro su gano waɗanda suka aikata shi tare da gurfanar da su a gaban shari'a.

  3. Yadda Kanawa ke murnar dawowar ruwan famfo

    Wasu al’ummun jihar Kano na murnar samun ruwan famfo a karon farko bayan fiye da shekara 10 wanda gwamnati ta kashe kimanin naira biliyan 22 don samarwa.

    Wasu daga cikin mutanen da ke murna sun bayyana mana farin cikinsu.

  4. An rufe makarantu kusan 500 kan zanga-zangar ɗalibai a Faransa

    Faransa na fara wani sabon makon karatu yayin da aka rufe makarantu kusan 500 sakamakon ci gaba da zanga-zangar da dalibai ke yi.

    Ministan Ilimi ya bayyana cewa an dauki matakin rufe makarantun ne saboda dalilai na tsaro, inda ya kara da cewa an kona ko kuma an yi mummunar barna a makarantu ashirin da hudu a cikin makonni uku na zanga-zangar.

    Daliban na cewa rashin malamai, da tsawon lokacin karatu a makaranta, da kuma rashin kayan aiki masu inganci na kawo cikas ga karatunsu.

    Wannan yunkuri ya samo asali ne daga wata makaranta a birnin Paris kafin daga bisani ya bazu zuwa sassan kasar baki daya.

  5. Ƴansanda sun gano sansanin da ake tsare da ƴan NYSC da aka sace

    Yan sanda a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya sun ce sun gano wani sansani da ake tsare da aƙalla matasa 19 masu yi wa ƙasa hidima da ƴanbindiga suka sace a baya-bayan nan.

    Kwamishinan ’yan sandan jihar, Audu Bosso, ya ce jirage marasa matuƙa sun taimaka wajen gano sansanin, amma jami’an tsaro ba su kai ga isa wajen ba saboda ana kyautata zaton an dasa abubuwan fashewa a zagayen wajen.

    Da yake magana da manema labarai ranar Asabar, Bosso ya ce: “Jiya mun shiga daji, mun bi sawunsu har zuwa wani wuri. Amma a lokacin ba mu iya kutsawa zuwa wurin da bayananmu suka nuna mana cewa suna can ba.”

    Ya ce binciken da aka yi da jirgi marar matuƙi ya tabbatar da inda sansanin yake.

    “Jirgin marar matuƙin ya nuna mana ainihin inda suke. Amma matsalar da muke fuskanta ita ce, bisa bayanan sirrin da muke da su, an dasa abubuwan fashewa a sansanin,” in ji Bosso.

    Ya ce ana tura motocin katapila da motocin yaƙi masu sulke yayin da ’yan sanda ke shirin gudanar da aikin ceto mutanen.

    Omotosho Adewale, wanda ɗansa ke cikin waɗanda aka sace, ya shaida wa BBC cewa kuɗin fansar da masu garkuwar ke nema sun fi ƙarfinsa.

    Ya ce “Naira miliyan 50 suke nema,”.

    Ya ƙara da cewa “Don Allah, duk abin da gwamnati za ta iya yi ta taimaka mani... Na samu damar rainon yaron nan ne kawai saboda taimako da goyon bayan da na samu daga kowa,”.

    Biyan kuɗin fansa abu ne da ya saɓawa doka a Najeriya, kuma hukumomi sun sha gargaɗin iyalan waɗanda aka sace kada su biya. Sai dai iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su kan fuskanci matsin lamba na biyan kuɗi domin a sako ’yan uwansu.

    Ba a bayyana takamaiman wurin da sansanin yake ba, kuma ’yan sanda ba su bayyana waɗanda ke da alhakin sace mutanen ba.

    Satar mutane domin neman kuɗin fansa na ci gaba da kasancewa babbar matsalar tsaro a Najeriya.

    A kudu maso gabashin ƙasar, an danganta wasu sace-sacen da aka yi a baya da ƙungiyoyin ƴan aware, ciki har da IPOB. Sai dai hukumomi ba su danganta wannan satar da wata ƙungiya ba.

    Lamarin ya jawo damuwa sosai, kasancewar sace mutane da yawa lokaci guda ba kasafai ake samun irin sa a kudancin Najeriya ba kamar yadda ake samu a wasu sassan arewacin ƙasar.

    Waɗanda aka sace sun taso ne daga Ibadan zuwa sansanin horas da masu yi wa ƙasa hidima a jihohin Abia da Akwa Ibom, lokacin da ’yan bindiga suka kai wa motocin bas ɗinsu hari kusa da Umunoha a jihar Imo a ranar Alhamis da ta gabata.

  6. Mun kai hare-hare 1,122 kan sansanonin Houthi - Yemen

    Wani mai magana da yawun dakarun da ke goyon bayan gwamnatin Yemen ya ce sun kai hare-hare 1,122 kan wuraren mayaƙan Houthi, ciki har da wuraren da aka girke manyan bindigogi, na'urorin harba rokoki da cibiyoyin bayar da umarni.

    A wata sanarwa da ya wallafa a shafin X, Majed Abdullah Nazili ya ce an kai hare-haren ne ta hanyar amfani da jiragen yaƙi, jirage marasa matuƙa, makamai masu linzami, rokoki, manyan bindigogi a lardunan Saada, Jawf da Taez, da kuma yankunan gabar tekun Yemen.

    Sanarwar ta kuma ce an kashe dakarun Houthi kusan 1,747 a hare-haren.

  7. Mutanen da Boko Haram ta kashe baya-bayan nan a Borno ya ƙaru zuwa 28

    Rahotanni daga Najeriya na cewa adadin mutanen da aka kashe sakamakon wani hari da Boko Haram ta kai a makon nan ya ƙaru zuwa 28.

    Boko Haram sun farwa mutanen ne lokacin da suka je yin ita ce.

    Wannan ne harin baya-bayan nan da aka kai a jihar Borno da wasu sauran jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalolin tsaro.

    Tun da farko an bayar da rahoton kashe mutum 15 da tuni aka yi jana'izarsu ranar Alhamis a ƙauyen Marte sai dai an sake gano wasu gawawwaki 13 a ƙarshen mako.

    Wata ƙungiya reshen IS da ke iƙirarin Jihadi tana da hannu a sace-sacen jama'a domin neman kuɗin fansa duk da tabbacin da gwamnatin ƙasar ke bayarwa cewa ana samun daidaito da kwanciyar hankali a yankin.

  8. Abubuwa 10 da ke kashe aure a arewacin Najeriya - Malamai

    A shekarun baya idan aka ji aure ya mutu a unguwa ko a gari akan shiga zulumi ko tambayar dalili bisa makomar miji ko matar ko 'ya'ya saboda rabuwar iyayensu.

    Sai dai yanzu zamani ya zo da sauyi ta yadda a wasu lokutan mutuwar aure bai zamo wani babban abin jimami ba, inda ake samun ma'aurata 'yan ƙasa da shekaru 30 aurensu yake mutuwa, a wani lokacin ma fiye da mutuwa daya, wani abu da masu lura da al'amuran yau da kullum ke ganin akwai firgici a cikinsa.

    Wata ƙididdiga ta Hukumar Hizba ta jihar Kano ta nuna cewar aƙalla gwamman aure ne ke mutuwa a wata guda, a jihar da tafi kowacce yawan al'umma a arewacin Najeriya.

    Malam Aminu Daurawa ya ce wannan ƙididdigar ta iya hukumar Hizba ce wadda kuma su aikinsu ya fi ƙarfi a gyaran aure da sulhu ga ma'aikata.

    Ya ce ba su da ƙididdigar kotu da ta ɓangaren fada, "kuma mafi yawan auren da ke mutuwa yana mutuwa ne a kotu".

    Wannan ne ya sa BBC ta tuntubi wasu malamai kuma masana zamantakewar rayuwa, wadanda suka haɗa da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Farfewa Mansur Isa Yelwa da kuma Dakta Abdallah Usman Gadon Ƙaya.

    Malaman uku sun yi ittifaƙin cewa dalilai 10 na janyo mutuwar aure ƙarƙashin rabe-rabe huɗu da suka hada da ta ɓngare miji da na ɓangren mata da na iyaye da 'yan uwa da kuma na al'umma.

    Karanta cikakken bayani a nan.

  9. Tsananin zafi na jefa masu juna biyu da jarirai cikin haɗari - MDD

    Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da batun sauyin yanayi ya yi gargadin cewa yanayin tsananin zafi na sanya mata masu juna biyu da jarirai cikin babban hadari.

    Wakiliyar BBC ta ce a cewar Simon Stiell, ana ƙara danganta tsananin zafi mai nasaba da sauyin yanayi da matsalolin haihuwa kafin lokaci, da haihuwar jaririai da suke zuwa babu rai, da kuma matsalolin lafiya ga uwa.

    Ana sa ran zai sanar da wakilai a wani taron sauyin yanayi a Fiji cewa sakamakon wani sabon bincike ya nuna cewa kusan kashi uku cikin huɗu na kwararru a fannin lafiyar mata masu juna biyu sun bayar da rahoton karuwar matsalolin lafiya da ke faruwa sakamakon tsananin zafi a cikin shekaru biyar da suka gabata.

  10. Amurka ta janye jiragen yaƙinta daga sansanin sojin saman Birtaniya

    Amurka ta janye dukkan jiragen yakinta masu jefa bama-bamai daga wani sansanin sojin sama a Ingila wanda aka yi zargin cewa an yi yunkurin kai wa hari.

    Ma'aikatar Tsaron Amurka Pentagon ba ta bayar da wani dalili na janyewar ba, amma wakilin BBC ya ce yadda aka yi janyewar ta ba-zata ya nuna alamun cewa akwai wani yanayi mai kama da fargaba a cikin lamarin.

    Wakilin BBC ya ce Amurka ta yi amfani da sansanin RAF Fairford wajen gudanar da hare-haren bam ta sama kan Iran ta hanyar amfani da jiragen B-1 da B-52, hare-haren da gwamnatin Birtaniya ta bayyana a matsayin na kare kai.

    A makon da ya gabata, hukumomin Birtaniya sun ayyana wani babban lamari bayan sun tare wasu motocin dakon kaya da ake ganin suna kan hanyarsu ce ta zuwa sansanin.

  11. Zaben shugaban ƙasa a Brazil zai shiga zagaye na biyu

    Zaɓen shugaban kasa a Brazil zai shiga zagaye na biyu, bayan da aka kasa samun wanda ya samu rinjayen kuri'u tsakanin Shugaba Lula da Silva da abokin hamayyarsa Flavio Bolsonaro.

    Mista Bolsonaro, wanda dan tsohon shugaban kasa Jair Bolsonaro ne da ke tsare a halin yanzu, zai shiga zagayen na biyu, wanda za a gudanar nan da mako uku, yana da tazarar da ba ta kai kashi biyu cikin dari ba a gaban abokin hamayyar nasa.

    Wakiliyar BBC ta ce Flávio Bolsonaro ya yi alkawarin yi wa mahaifinsa, da magoya bayansa da suka kai hari kan gine-ginen gwamnati bayan shan kaye a zabe, afuwa daga hukuncin da suke fuskanata a halin yanzu.

    Shugaba Lula dai ya bayyana sakamakon zaben a matsayin wanda ba a yi tsammaninsa ba, amma ya kara da cewa a shriye ya ke ya tunkari zagaye na biyu.

  12. Marabanku

    Masu bin mu a wannan shafi na BBC Hausa kai-tsaye, barkan mu da safiyar wannan rana ta Litinin – tushen aiki.

    Nabeela Mukhtar Uba ke fatan kasancewa da ku a wannan shafi, domin kawo irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya, musamman Najeriya da makwabtan ƙasashe.

    Kuna iya tofa albarkacin bakinku kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta: facebook; X, Instagram, har ma da Youtube.