Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 12/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 12/11/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • INEC
  • Atiku
  • Shugaba Tinubu
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Hoto
  • Ƴar Arewan da ke buga wa Najeriya ƙwallo
  • waya
  • Gwamna Adeleke na Accord
  • Jihohi masu talauci
  • Buba Galadima

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Muslim Muhammad Yusuf

  1. APC ta yi Allah-wadai da hare-haren da ake kai wa tarukan jam’iyyun adawa

    APC

    Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi Allah-wadai da hare-haren da ake kai wa tarukan siyasa na jam’iyyun adawa a wasu sassan ƙasar, inda ta buƙaci jami’an tsaro su kama waɗanda ke da hannu a hare-haren.

    A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar, Dele Alake ya fitar, APC ta ce ta lura da ƙaruwar hare-haren da ake kai wa tarukan siyasa a sassan ƙasar.

    Jam’iyyar ta ce hare-haren da aka ruwaito a jihohin Edo, Cross River da Gombe, da sauran waɗanda aka kai wa magoya bayan jam’iyyu da shugabannin siyasa, abin Allah-wadai ne.

    Ta kuma yi Allah-wadai da tarwatsa taron tattaunawa da aka shirya yi a yau Alhamis na jam’iyyar NDC a Legas.

    APC ta yi kira ga jam’iyyun siyasa, ’yan siyasa da magoya bayansu da su kame kansu, tare da guje wa duk wani abu da ka iya haddasa rikici da tarzoma a cikin al’umma yayin da ake ci gaba da kamfen.

    Ta kuma buƙaci jami’an tsaro su ƙara kaimi wajen hana duk wani nau’in tashin hankali da ya shafi siyasa, tare da tabbatar da kama waɗanda ke haddasa hare-haren da waɗanda ke aikata su, domin hukunta su bisa tanadin doka.

  2. Mutane takwas sun mutu bayan ginin bene ya rufta a New York

    New York

    Mutane takwas ne suka mutu, yayin da wasu akalla 17 suka jikkata bayan wani gini ya rufta a birnin New York na Amurka a yammacin Laraba, kamar yadda magajin garin, Zohran Kwame Mamdani, ya bayyana.

    Mamdani ya ce jami'an ceto sun ci gaba da aikin neman waɗanda suka makale a ƙarƙashin baraguzan ginin cikin dare, duk da haɗarin da ke tattare da aikin. Daga cikin waɗanda suka jikkata akwai jami'an kashe gobara uku.

    A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, magajin garin ya bayyana alhininsa kan asarar rayukan, tare da miƙa ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu da kuma waɗanda suka jikkata.

    Har yanzu ana ci gaba da aikin ceto, yayin da hukumomi suka buƙaci jama'a su guji zuwa wurin domin ba jami'an agaji damar gudanar da aikinsu.

    Mamdani ya kuma buƙaci duk wanda ya kasa samun labarin 'yan uwansa ko abokansa da ake fargabar suna cikin waɗanda lamarin ya shafa da ya tuntubi hukumomin agajin gaggawa.

    Hukumomi sun ce har yanzu suna gudanar da bincike domin gano musabbabin ruftawar ginin, yayin da ake fargabar akwai wasu mutanen da suka makale a ƙarƙashin baraguzan ginin.

    Wasu ganau sun bayyana yadda suka shiga firgici lokacin da ginin ya rufta da misalin ƙarfe 10 na dare agogon yankin a ranar Laraba.

  3. An sallami matar da ta shiga Najeriya da cutar Ebola daga asibitin Switzerland

    Ebola

    An sallami matar nan 'yar Uganda mai shekaru 42 da ta zama mutum ta farko da aka tabbatar ta kamu da cutar Ebola a Najeriya cikin sama da shekaru 10, daga wani asibiti a Switzerland bayan ta warke sarai.

    Asibitin Geneva University Hospitals ya ce an sallame ta ne a ranar Alhamis bayan likitoci sun tabbatar da cewa ta warke gaba ɗaya.

    An fitar da matar daga Abuja zuwa Switzerland a ranar 26 ga watan Oktoba domin yi mata magani, tare da mijinta, wanda wani jami'in diflomasiyyar Switzerland ne, saboda an bayyana cewa ya yi mu'amala ta kusa da ita.

    Matar ta kamu da cutar Ebola nau'in Bundibugyo, inda aka tabbatar da hakan a ranar 20 ga watan Oktoba.

    Hukumomin Switzerland sun ce babu barazanar yaɗuwar cutar ga sauran al'umma sakamakon zuwanta ƙasar domin neman magani.

    Sun kuma ce ba a sanya wani takunkumin shiga ƙasar ga sauran jama'a ba saboda barkewar cutar.

    Asibitin ya ce ba zai sake fitar da wasu bayanai game da matar ba domin kiyaye sirrinta.

    A halin da ake ciki, ana sa ran Najeriya za ta iya ayyana cewa ta kawar da ɓarkewar cutar Ebola tun daga ranar 7 ga watan Disamba, idan ba a samu wani sabon wanda aka tabbatar ko ake zargin ya kamu da cutar ba.

    Ministan Lafiya na Najeriya, Muhammad Ali Pate, ya ce an fara bibiya na tsawon kwanaki 42 da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tanada tun bayan tafiya da matar zuwa Switzerland a ranar 26 ga watan Oktoba.

  4. Mutane miliyan 29 na fuskantar yunwa a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo

    DRC

    Kimanin mutane miliyan 28.8 ne ke fuskantar tsananin ƙarancin abinci a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, kamar yadda wani sabon rahoto da gwamnati da hukumomin agaji suka fitar ya nuna.

    Binciken da shirin tantance matsalar ƙarancin abinci (IPC) ya gudanar ya nuna cewa kashi 23 cikin 100 na al'ummar ƙasar ne ke fuskantar matsalar tsakanin watan Satumba zuwa Disamban 2026.

    Rahoton ya ce mutane miliyan 3.6 na cikin mummunan yanayin ƙarancin abinci, inda gabashin ƙasar, musamman lardunan arewaci da kudancin Kivu da Ituri, suka fi fuskantar matsalar.

    Sama da mutane miliyan 10 a waɗannan yankuna na cikin mawuyacin hali ko fiye da haka.

    Mukaddashin jami'in kula da ayyukan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasar, Damien Mama, ya bayyana sakamakon binciken a matsayin abin damuwa, yana mai cewa buƙatun agaji na ƙaruwa yayin da kuɗaɗen gudanar da ayyukan agajin ke raguwa.

    A nasa ɓangaren, babban sakataren ma'aikatar noma ta ƙasar, Benjamin Toirambe Bamoninga, ya ce binciken zai taimaka wajen tsara hanyoyin tallafa wa al'umma da kuma bunƙasa samar da abinci.

    Binciken ya kuma yi hasashen cewa matsalar za ta ƙara tsananta tsakanin watan Janairu zuwa Yunin 2027, inda ake sa ran mutane miliyan 30.3 za su fuskanci ƙarancin abinci mai tsanani, ciki har da miliyan 4.2 da za su shiga matakin gaggawa.

    Rahoton ya danganta matsalar da rikice-rikicen tsaro, tilasta wa mutane barin muhallansu da kuma matsin tattalin arziki.

  5. Shugaban kamfanin Nvidia ya yi murabus bayan zargin mu'amala da mata

    Nividia CEO

    Shugaban kamfanin fasahar kwamfuta na Nvidia, Jensen Huang, ya yi murabus daga muƙaminsa.

    Kwamitin gudanarwar kamfanin ya sanar da murabus ɗin, tare da yaba wa gudummawar Huang wajen bunƙasa kamfanin, yana mai cewa ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gabansa.

    A baya-bayan nan dai, Huang ya fuskanci wasu zarge-zarge bayan rahotannin da suka bayyana cewa ya yi hulɗar soyayya da wata 'yar China mai suna Alice Huang, wadda jami'an leƙen asirin Amurka ke zargin tana yi wa gwamnatin China leƙen asiri.

    Rahotannin sun kuma nuna cewa Huang ya yi wata hulɗar soyayya da wata babbar ma'aikaciyar kamfanin Nvidia mai suna Kimberly Powell, wadda take ƙarƙashinsa a wurin aiki.

    Huang ya amince cewa ya ci amanar matarsa, tare da neman afuwa ga iyalinsa da ma'aikatan kamfanin.

    ...

    Kwamitin ya kuma sanar da naɗa Colette Kress, wadda a baya take mataimakiyar shugaban kamfanin kuma babbar jami'ar kula da harkokin kuɗi, a matsayin shugabar riƙo.

    Harvey Jones, wanda aka zaɓa a matsayin shugaban kwamitin gudanarwar kamfanin na farko, ya ce Kress ta taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasar Nvidia, kuma tana da cikakken masaniya kan ayyukan kamfanin da harkokin kuɗinsa.

    Kress za ta jagoranci kamfanin na ɗan lokaci yayin da ake ci gaba da neman sabon shugaba na dindindin.

    A nata ɓangaren, ta ce kamfanin zai ci gaba da ƙoƙarin da ya sanya shi kan gaba a fannin fasahar kwamfuta da ke amfani da basirar na'ura mai ƙirƙira (AI).

  6. An ji ƙarar harbe-harbe a kusa da fadar White House

    ...

    Aƙalla mutane biyar ne suka jikkata sakamakon harbe-harbe da aka yi a tsakiyar birnin Washington, DC na ƙasar Amurka.

    'Yan sanda sun ce lamarin ya faru ne a titin 15th da P Streets, a yankin arewa maso yammacin birnin, a cikin wani ɗakin motsa jiki da kuma kusa da shi.

    A cewar rundunar 'yan sandan Washington DC, lamarin ya haifar da wani yanayi mai tayar da hankali, inda wani mutum ko wasu mutane suka kulle kansu a cikin ginin.

    An tura jami'an agajin gaggawa zuwa wurin da lamarin ya faru, yayin da 'yan sanda ke kira ga mazauna yankin da su guji zuwa wurin.

    Jami'an 'yan sanda sun ce har yanzu ba su san halin da mutanen biyar da aka harba suke ciki ba.

    Wani ganau ya ce da farko ya yi tunanin ƙarar da ya ji ta fito ne daga fashewar ƙwallon motsa jiki, kafin daga bisani ya fahimci cewa an harbi wani mutum.

    ...
  7. Ghana ta sabunta takardun kuɗinta na Cedis

    Ghana Cedis

    Babban Bankin Ghana ya sanar da cewa zai fara fitar da sabbin takardun kuɗin ƙasar domin amfani da su tun daga watan Disamba mai zuwa.

    A cewar babban bankin, sabbin takardun kuɗin na cedi sabunta fasali ne na takardun kuɗin da ake amfani da su a yanzu, waɗanda har yanzu za su ci gaba da kasancewa halastattun kuɗaɗen mu'amala.

    An sanya wa sabbin takardun kuɗin suna "Heritage Series".

    Babban bankin ya ce an shafe fiye da shekara 20 ana amfani da zane da fasalin takardun kuɗin da ake da su a yanzu, lamarin da ya sa hukumomi suka ga lokaci ya yi da za a sake fasalta su.

    A halin yanzu, Ghana na da nau'o'in takardun kuɗi takwas: cedi 1, cedi 2, cedi 5, cedi 10, cedi 20, cedi 50, cedi 100 da kuma cedi 200.

    Sabbin takardun kuɗin za su kasance cikin waɗannan nau'o'i ne.

    Sai dai babban bankin ya bayyana cewa ba zai ƙirƙiro wani sabon nau'in takardar kuɗi ba.

  8. Mayaƙan Houthi sun kai hari Aden na ƙasar Yemen

    Houthi

    Majiyoyin tsaro na gwamnatin Yemen da ke samun goyon bayan Saudiyya sun ce 'yan tawayen Houthi sun kai hare-hare a ranar Laraba a birnin Aden, inda gwamnatin ke gudanar da harkokinta.

    A cewar majiyoyin, hare-haren sun kai hari ne kan sansanonin sojojin gwamnati.

    Tun da fari, dubban mutane sun hallara a babban birnin ƙasar, Sana'a, wanda ke ƙarƙashin ikon Houthi, domin halartar jana'izar mutane da dama da aka kashe a makon da ya gabata a hare-haren da aka bayyana a matsayin na Saudiyya.

    Yaƙin Yemen dai ya shafe sama da shekara goma yana gudana, tun bayan da ƙungiyar Houthi ta ƙwace ikon babban birnin ƙasar, Sana'a, a shekara ta 2014.

    A shekara ta 2015, wata ƙawancen ƙasashe da Saudiyya ke jagoranta ta shiga yakin domin mara wa gwamnatin Yemen baya.

    Wata yarjejeniyar tsagaita wuta mai rauni da ɓangarorin suka cimma a shekarar 2022 ta rushe a watan Yuli.

    Tun daga lokacin ne rikicin tsakanin Saudiyya da mayaƙan Houthi ya ci gaba.

    A cikin wannan lokaci, mayaƙan Houthi sun kai hare-hare kan filayen jiragen sama da cibiyoyin makamashi da kuma sansanonin sojin Saudiyya.

  9. Harin Isra'ila a asibitin Gaza ya kashe mutum shida

    Jami'an Falasɗinawa sun ce wani harin sama da Isra'ila ta kai kan babban asibitin kudancin Gaza ya kashe mutane shida, ciki har da wani likitan fiɗa, tare da jikkata sama da mutum ashirin.

    Hotunan bidiyo sun nuna mummunar barna da aka yi wa ɗakin tiyata da kuma wurin kwanan ma'aikatan lafiya a Asibitin Nasser, ɗaya daga cikin ƙalilan cibiyoyin kiwon lafiya da har yanzu suke aiki a Gaza.

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kai harin ne kan wani "babban ɗan ta'addan Hamas", tare da zargin cewa ana amfani da asibitin a matsayin "cibiyar umarni", ba tare da bayar da wata hujja ba.

    Isra'ila ba ta ba wa 'yan jarida na ƙasashen waje izinin shiga Gaza domin su ba da rahoto kai tsaye da kansu kan abin da ke faruwa a wurin.

    Asibitoci na da kariya a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa, amma Isra'ila ta sha kai hare-hare a kansu a matsayin martani kan hare-haren Hamas na shekarar 2023.

  10. Amurka ta samu nasarar da take buƙata a yaƙin Iran - Trump

    Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Amurka ta yi nasara a yaƙin da ta yi da Iran, sai dai ya ce batun yaushe rikicin zai kare wani abu ne na daban.

    Da yake jawabi a wajen bikin Ranar Tsofaffin Sojoji da aka gudanar a maƙabartar Arlington National Cemetery da ke jihar Virginia, Trump ya ce ba ƙasarsa ce ta fara yakin ba.

    "Ba Amurka ce ta fara yaƙi da Iran ba. Iran ta kasance cikin gaba da Amurka tun daga shekarar 1979. Ya kamata a ce an warware wannan batu tun tuni."

    "A ƙarƙashin gwamnatinmu ta yanzu ne, a ƙarshe lokaci ya yi da wani ya tsaya musu. Dukkanmu mun mayar da martani. Mun rama kuma mun yi martani mai karfi. Kuma mun yi nasara'', in ji shi.

    Ya ƙara da cewa abin da ya rage shi ne tambayar lokacin da ake son kawo ƙarshen lamarin.

    ''Muna son tabbatar da cewa mun samu cikakkiyar nasara, ba nasarar kashi 93 cikin 100 ba. Zai kasance cikakkiyar nasara''.

    "Zai dauki shekaru 25 ana sake gina abin da muka lalata, kuma muna fatan ba za mu sake lalata wani ɓangare na waccan ƙasar ba." in ji Trump.

  11. Wakilan Amurka za su gana da Putin a Moscow

    Wakilan Shugaba Trump na musamman - Jared Kushner da Steve Witkoff - za su gana da Shugaba Vladimir Putin a birnin Moscow.

    Matakin na zuwa ne bayan sun shiga tsakani a tattaunawar kwana biyu tsakanin wakilan Rasha da na Ukraine a birnin Abu Dhabi.

    Ana sa ran wakilan na Amurka za su gabatar da shawarar faɗaɗa tattaunawa kan yaƙin na Ukraine, ta yadda za a sanya wakilan ƙasashen Turai a ciki.

    Ya zuwa yanzu, Rasha ba ta nuna sha'awar karɓar wannan shawara ba.

    Daga nan, wakilan biyu za su nufi ƙasar Ireland domin ganawa da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, wanda a baya ya shaida wa manema labarai cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen samun ci gaba a kan cimma yarjejeniya a cikin wannan shekarar.

  12. Za a ƙwalla rana a arewacin Najeriya - NiMet

    Wasu mutane

    Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi hasashen ƙwalla rana a jihohin arewacin Najeriya.

    Cikin wata sanarwar da ta fitar a shafinta na X, NiMet ta ce za a ƙwalla rana mai zafi a jihohin arewacin Najeriya a ranar Alhamis, 12/11/2026.

    ''Da safiyar wannan rana ana hasashen samun yanayi na bushi da zafin rana a ilahirin yankin'', in ji sanarwar.

    Haka kuma NiMet ta ce wannan yanayi zai ci gaba da ƙaruwa a lokacin da rana ta take, har zuwa yammacin wannan rana.

    Kan haka ne hukumar ta shawarci mazauna yankin su ɗauki matakin kauce wa shigar ranar domin rage hatsarin fuskantar illar ranar.

  13. Iran ta sake yin barazanar kashe Trump da Netanyahu

    Kioumars Heydari

    Mataimakin babban hafsan sojin Iran, Birgediya Janar Kiomars Heidari ya yi barazanar kashe shugabannin Amurka da Isra'ila a wata hira da ya yi a kafar talabijin.

    "Za mu kashe Trump da Netanyahu," in ji babban sojan a cikin wani bidiyo da kamfanin dillancin labaran Iran ya wallafa ranar Laraba.

    A cikin tattaunawar, babban jami'in sojan na Iran ya yi iƙirarin cewa Amurka ta girke jiragen ruwanta na yaƙi a wurin da bai fi nisan kilomita 500 ba daga gaɓar Iran.

    Wannan lamari na zuwa ne bayan da Iran ta kai farmaki kan wasu jiragen ruwan sojin Amurka biyu a ranakun 6 da 7 ga watan Satumba.

    Birgendiya Janar Heidari ya yi iƙirarin cewa a artabun da aka samu na baya-bayan nan tsakanin Iran da Amurka, dakarun Iran sun yi nasarar lalata jiragen yaƙin Amurka 300, sannan sun yi amfani da fasahar zamani wajen kama wasu jiragen.

    Haka nan ya bayyana cewa akwai wasu ɓoyayyun makaman yaƙi na Iran waɗanda ƙasar ke shirin amfani da su matuƙar yaƙin ya tsawaita.

  14. Tinubu ya gode wa sarkin Gwandu kan bai wa ɗansa sarauta

    Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya ɗansa, Seyi Tinubu, murnar samun sarautar Ɗan Zakin Gwandu.

    A ranar Laraba ne Mai Martaba Sarkin Gwandu a jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, ya naɗa Seyi sarautar a fadarsa.

    Cikin wta sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar, Tinubu ya gode wa Sarkin Gwandu da Majalisar Masarautar Gwandu bisa wannan karramawa, wadda Sarkin ya ce ita ce irinta ta farko a tarihin masarautar.

    ''Wannan karramawa ta zarce girmama mutum kaɗai, domin tana nuna dangantakar abota, mutunta juna da kuma haɗin kai da ke tsakanin al'ummomin Najeriya mabambanta'', in ji shi.

    "A matsayina na uba, ina farin cikin ganin an karrama ɗana daga wata fitacciyar masarauta mai dogon tarihi'', in ji Shugaba Tinubu.

    ''Don haka ina gode wa Sarkin Gwandu da mutanen Jihar Kebbi bisa wannan girmamawa da suka yi wa ɗana."

    Ya kuma yabawa ƙoƙarin Seyi wajen hulɗa da matasa, bunƙasa al’umma da kuma ƙarfafa gwiwar jama'a, musamman ta hanyar rawar da yake takawa a ƙungiyar City Boy Movement da sauran shirye-shiryen tallafa wa matasan Najeriya.

    "Sarautar Dan Zaki Gwandu na ɗauke da darajoji irin su jarumtaka, shugabanci da hidima. Ina ƙarfafa shi ya yi rayuwa bisa waɗannan darajoji, ya ci gaba da zama mai tawali'u, kuma ya sadaukar da kansa wajen kyautata rayuwar al'umma.''

    Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci Seyi da ya ɗauki wannan sarauta a matsayin kira na ƙara zage damtse wajen bayar da gudunmawa ga ci gaba, zaman lafiya da kuma yi wa Najeriya hidima.

  15. An kama tsohon babban alƙali da zargin safarar ƙwaya

    An kama wani tsohon babban alkali a ƙasar Bolivia bisa zargin safarar miyagun kwayoyi, bayan da Amurka ta sanya sunansa a jerin mutanen da ta haramta mu'amala da su.

    An kama Aldo Quezada a gidansa da ke birnin Santa Cruz, a gabashin asar.

    A watan da ya gabata ne ya yi murabus daga muƙaminsa na babban alƙali a kotun yankin.

    Shi ne mutum na baya-bayan nan daga ɓangaren shari'a da ya shiga cikin jerin waɗanda ake gudanar da bincike a kansu, saboda zargin suna da alaƙa da ƙungiyoyi masu aikata manyan laifuka.

    A farkon wannan watan, babban alƙalin Kotun Kolin Bolivia da iyalansa sun tsere daga ƙasar, inda suka zargi shugaban ƙasa, Rodrigo Paz—wanda ke samun goyon bayan Amurka - da yunƙurin gallaza masa da kuma yi masa barazana.

  16. An kafa sabon tarihi a siyasar Amurka

    Trump

    Jam'iyyar Democrat ta sake samun wani babban nasara a zaɓen tsakiyar wa'adi na Amurka - inda aka sanar da Scott Colom a matsayin wanda ya lashe zaɓen majalisar dattawa a jihar Mississippi.

    Sakamakon—wanda aka sanar mako guda bayan zaɓen—ya nuna cewa ya samu nasara da tazara kaɗan a kan Cindy Hyde-Smith, 'yar jam'iyyar Republican wadda ke riƙe da kujerar.

    Wannan dai shi ne karo na farko da jihar ke zaɓar ɗan jam'iyyar Democrat cikin kusan shekara 40.

    Mista Colom ya gudanar da yaƙin neman zaɓensa ne kan tsadar rayuwa inda ya caccaki sanata Cindy Hyde-Smith kan kalaman da ta yi da ke nuna ta yi watsi da halin da mutane ke ciki.

    Sabon zaɓaɓɓen ɗan majalisar dattawan ya zama baƙar fata na farko da ya lashe muƙamin siyasa a matakin jiha a Mississippi, tun shekarun da suka biyo bayan Yaƙin Basasar Amurka.

  17. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.