Libya ta haramta sanya tufafin da ke ɗauke da tambarin Nike

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Hukumar ba da fatawa mafi girma a Libya ta fitar da fatawa da ta haramta wa Musulmi saye, sayarwa ko sanya tufafin da ke ɗauke da tambarin kamfanin kayan wasanni na Nike.
Dar al-Ifta ta ce yin hakan na nufin inganta bautar gumaka, domin shahararren tambarin kamfanin mai siffar lanƙwasa (swoosh) an ce an samo shi ne daga fikafikan Nike, allahiyar nasara a tatsuniyoyin Girka, wadda kamfanin ya karɓi sunanta.
Hukumar ta kuma zargi kamfanin da goyon bayan Isra'ila.
Sai dai wannan fatawa ba doka ba ce da za a tilasta aiwatarwa, kuma ba ta fayyace hukuncin da za a ɗauka kan waɗanda suka karya umarnin ba.































