Iran za ta rasa abin sayarwa nan da makonni biyu – Amurka
Sakataren baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya ce Iran za ta iya rasa dukkan kayayyakin da take da su na sayarwa ko musayar kasuwanci cikin makonni masu zuwa, sakamakon matakan da Washington ke ɗauka kan tattalin arziƙin ƙasar.
Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Fox News, Bessent ya ce Iran na da gangar ɗanyen mai miliyan 15 kacal da ke kan ruwa, kuma ana sa ran za ta kai jigilar mai ta ƙarshe zuwa China cikin makonni biyu masu zuwa.
Ya ce: “Iran ba ta da wani abin da za ta iya sayarwa. Wataƙila cikin makonni biyu masu zuwa za ta kai jigilar mai ta ƙarshe, bayan haka kuma ba za ta samu komai ba.”
A baya, Bessent ya ce Amurka za ta aika da tawagogi zuwa wasu ƙasashe domin matsa musu su dakatar da kasuwanci da Tehran.































