KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 19/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 19 ga watan Agusta, 2026.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello, Haruna Kakangi

  1. Kotu za ta yanke hukuncin kan yunkurin korar ƴar Najeriya daga Afirka ta Kudu

    Chidinma Adetshina

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Chidinma Adetshina

    Ana sa ran cewa wata kotun yankin Cape Town za ta yanke hukunci a yau game da batun Chidinma Adetshina, ƴar Najeriyar da ta lashe sarauniyar kyau a shekarar 2024, bisa yunkurin hukumomi na mayar da ita Najeriya.

    A watan Yuni ne aka kama Chidinma bayan ta sake shiga Afirka ta Kudu ta kan iyaka da Mozambique.

    Lamarin ya biyo bayan taƙaddama da aka samu game da zaman ta ƴar asalin ƴar Afirka ta Kudu.

    An haifi Chidinma ne a ƙasar ta Afirka ta Kudu, inda mahaifiyarta ƴar ƙasar ce yayin da mahaifinta ɗan Najeriya ne.

    Sai dai taƙaddama ta kaure game da asalinta bayan da ta cancanci zuwa matakin ƙarshe na zaɓen sarauniyar kyau ta Afirka ta Kudu a shekarar 2024.

    Lauyan da ke kare ta na ƙalubalantar tsare ta da aka yi da kuma yunƙurin fitar da ita daga ƙasar yayin da ma'aikatar harkokin cikin gida ta Afirka ta Kudu ta ce ba ta da halastattun takardun ci gaba da zama a ƙasar.

  2. An fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    Yau ce ranar farko ta fara yaƙin neman zaɓe a Najeriya gabanin babban zaɓen ƙasar na watan Janairu, yayin da ake nuna damuwa kan matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa da kuma tsadar rayuwa a ƙasar.

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu na neman wa'adi na biyu sai dai farin jininsa ya yi ƙasa a baya-bayan nan.

    Ɗaya daga cikin manyan ƴan adawa mafi ƙarfi da ke takara da Tinubu shi ne tsohon shugaban ƙasar Atiku Abubakar, sai kuma tsohon gwamna Peter Obi.

    Bankin Duniya ya ce sama da rabin ƴan Najeriya na rayuwa cikin ƙangin talauci.

  3. Iran ta gargaɗi ƙasashen yankin Gulf kan haɗa kai da Amurka

    Babban hafsam sojin Iran

    Asalin hoton, Tasnim

    Rundunar sojin Iran ta gargaɗi ƙasashen yankin Gulf kan haɗa kai da Amurka wajen shirya mata hare-hare.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa X, babban hafsan rundunar sojin ƙasar Iran, Ali Abdollahi ya ce "Ba zai yiwu a jibge ɗimbin jiragen yaƙi, musamman jiragen ɗaukar mai, a yankin ba tare da ƙasashen sun sun sani ba."

    Ya ce Iran za ta ɗauki duk wani "taimako" da aka bai wa sojojin Amurka a matsayin haɗa kai ko bayar da goyon baya ga dakarun Amurka.

    A tsawon lokacin yaƙi tsakanin Iran da Isra'ila tare da Amurka, Iran ta kai hare-hare sau da dama kan sansanonin soji da ke ƙasashen yankin waɗanda ke ƙawance da Amurka.

  4. Laberiya ta amince ta karɓi baƙin da Amurka ta kora

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    Laberiya ce ƙasar Afirka ta baya-bayan nan da ta amince ta karɓi baƙin da Amurka ta kora, inda ake sa ran irin waɗannan baƙi guda 20 za su isa ƙasar gobe Alhamis.

    Gwamnatin Laberiya ta ce ta amince ta karɓi baƙin da suka kai 1,200 a ƙarƙashin shirin Amurka na tura baƙin da ta kora zuwa wasu ƙasashe na daban.

    A watan Satumban bara, gwamnatin Laberiya ta amince ta karɓi baƙi waɗanda ƴan asalin ƙasashen Afirka ne da kuma ƴan asalin ƙasashen yankin nahiyar arewaci da kudancin Amurka na shekara ɗaya, bisa dalilai na jin-ƙai.

    Ma'aikatar yada labarai ta ƙasar ta fitar a wata sanarwa cewa ba za a bai wa ƙasar wata lada ba a sanadiyyar hakan sai dai za a taimaka mata wajen tabbatar da samun nasarar shirin da kuma ƙarfafa harkar shige da ficenta.

    Haka nan kuma gwamnatin ƙasar ta Laberiya ta ce za a bai wa baƙin damar neman mafaka a ƙasar idan suna buƙata, kuma za su iya ci gaba da zama a ƙasar idan suna son hakan.

    Aƙalla ƙasashen Afirka 10 ne suka amince su karɓi baƙin da Amurka ta kora a ƙarƙashin shirin gwamnatin Donald Trump na tura baƙi zuwa wasu ƙasashe na daban.

    A mafi yawan lokuta babu cikakken bayani kan irin waɗannan yarjeniyoyi tsakanin Amurka da ƙasashen, sai dai wasunsu sun karɓi ladan kuɗaɗe. Misali, Eswatini ta karɓi kuɗi sama da dala miliyan biyar kan karɓar irin waɗannan baƙin.

  5. Iran ta musanta harba wa Daular Larabawa makamai

    Mojtaba Khamenei

    Asalin hoton, TASNIM

    Bayanan hoto, Jagoran addini na Iran Mojtaba Khamenei

    Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin waje ta Iran ya musanta zargin da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta yi na cewa Iran ɗin ta harba mata makamai masu linzami.

    Ismael Beqai ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa “zargin na UAE ba shi da tushe balle makama”.

    Mai Magana da yawun na Iran ya ce: “Matakin na Háɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya saɓa da tsarin zama na maƙwaftaka kuma hakan zai iya yin cikas ga yunƙurin da ake yi na yayyafa wutar rikici tsakanin ƙasashen yankin.”

    Sa’o’i bayan Iran ta sanar da cewa ta harba makamai ne ƙasar ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ce ta dakatar da duk wata alaƙa ta kasuwanci ko kuɗi da Iran har sai abin da hali ya yi.

    Tun bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin Iran da Amurka, Daular Larabawa ta kasance ƙasar da ta fi shan hare-hare daga Iran a yankin.

  6. Ruftawar mahaƙar ma'adanai ta kashe mutum 107 a Kamaru

    Shugaban ƙasar Kamaru Paul Biya

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban ƙasar Kamaru Paul Biya

    Aƙalla mutum 107 sun mutu sanadiyyar ruftawar ramin haƙar ma'adanai a ƙauyen Zamboi da ke kan iyakar Kamaru da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, kamar yadda wani jami'i a yankin ya bayyana wa BBC.

    Adamou Abdon, wanda shi ne magajin garin Garoua-Boulai a yankin gabashin Kamaru ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata.

    "An zaƙulo gawarwaki 107 daga cikin ƙasa," kamar yadda ya shaida wa BBC, inda ya ƙara da cewa lamarin "ya faru ne a wani wurin haƙar ma'adanai da ke bangaren Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, kusa da kan iyaka da ƙasar Kamaru."

    Har yanzu babu tabbas kan abin da ya haddasa ruftawar ƙasar. Bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda ƙasa ta rufta kan masu haƙar zinare da ke a mahaƙar.

    Ana ƙoƙarin gudanar da aikin ceto a yankin sannan ana fargabar cewa yawan waɗanda suka mutu zai ƙaru.

    Haƙar ma'adanai ɗaya ne daga cikin manyan hanyoyin dogaro na mutanen gabashin Kamaru.

    Sai dai babu yanayi mai kyau a wuraren haƙar ma'adanan, inda a mafi yawan lokuta masu aikin kan fada cikin haɗarin kamuwa da cutuka ko kuma bala'o'i.

    Haka nan kuma ruftawar wuraren haƙar ma'adanai abu ne da ya yawaita a ƙasar.

  7. Tsohon ministan tsaron Ukraine na son a yi sabon zaɓe a ƙasar

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, na fuskantar ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen siyasa ga ikonsa tun bayan fara mamayar da Rasha ta kai wa ƙasar, bayan da tsohon ministan tsaronsa ya yi kira da a gudanar da zaɓe.

    Mykhailo Fedorov, wanda aka kora daga muƙaminsa a watan da ya gabata lamarin da ya haifar da zanga-zanga a sassa daban-daban na ƙasar, ya ce bai kamata dimokuraɗiyya ta zama abin da Rasha za ta iya dakatarwa ba.

    Sai dai dokar ta-ɓaci da ake aiwatarwa a Ukraine tun bayan fara yaƙi har yanzu ta haramta gudanar da zaɓe a lokacin da ake fama da yaƙi.

    Har zuwa yanzu, Shugaba Zelensky bai mayar da martani a hukumance kan kiran da Fedorov ya yi ba. A gefe guda kuma, sojojin Ukraine na ci gaba da kai hare-hare a cikin yankunan Rasha.

    Gwamnan yankin Bashkortostan na Rasha, Radiy Khabirov, ya ce wasu jiragen sama marasa matuƙa na Ukraine sun haddasa gobara a wani wurin masana'antu da ke yankin.

  8. Barka da warhaka!

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce za ta kasance da ku daga yanzu zuwa ƙarfe 4 na yamma in sha Allah.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.