Hotunan yadda Aisha Buhari ta karrama 'yan fim

An wallafa

Uwargidan Shugaban Najeriya Aisha Buhari ta karrama wasu 'yan wasan Hausa da mawaka da kuma masu shirya fina-finai daga yankin arewacin kasar.

Kannywood
Bayanan hoto, Uwargidan Shugaban Najeriya Aisha Buhari ta karrama wasu 'yan wasan Hausa da mawaka da kuma masu shirya fina-finai daga yankin arewacin kasar
Kannywood
Bayanan hoto, An gudanar da taron liyafar ne a Abuja ranar Laraba
Kannywood
Bayanan hoto, Cikin 'yan wasan da aka karrama har da jaruma Fati Washa
Kannywood
Bayanan hoto, Adam A Zango yana cikin 'yan wasan Hausa da suka nishadantar da su
Kannywood
Bayanan hoto, Jaruma Maryam Yahaya ita ma ta samu lambar yabo lokacin taron
Kannywood
Bayanan hoto, Shugaba Muhammadu Buhari wanda shi ma ya halarci taron ya shiryawa 'yan wasan irin wannan liyafar kimanin makonni biyu da suka wuce
Kannywood
Bayanan hoto, Aisha Buhari ta shirya masu liyafar ne don kaddamar da wata sabuwar wakar kamfe din Buhari a zaben 2019 wadda aka wa lakabi da 'Sakamakon Chanji'
Kannywood
Bayanan hoto, Cikin 'yan wasan da aka karrama har da Hannatu Bashir da sauransu
Kannywood
Bayanan hoto, Hauwa Waraka ma tana cikin jaruman da suka karbi lambar yabo lokacin taron
Kannywood
Bayanan hoto, Jaruma Fati Shu'uma ta samu lambar yabo
Kannywood
Bayanan hoto, Har ila yau mawaka kamarsu Ado Gwanja da Naziru M Ahmed sun halarci taron