Kalli hotunan ganawar Buhari da 'yan Kannywood

An wallafa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wasu 'yan wasan Hausa da mawaka da kuma masu shirya fina-finai daga yankin arewacin kasar a fadar da ke Abuja.

Shugaba Buhari
Bayanan hoto, Shugaba Buhari ya shirya wa 'yan wasan Hausan liyafar ne a ranar Alhamis
Shugaba Buhari
Bayanan hoto, 'Yan wasan sun ba shi tabbacin samun goyon bayansa a babban zaben kasar wanda za a yi a shekarar 2019
Buhari
Bayanan hoto, Cikin 'yan wasan da suka halarci taron har da Rukayya Dawayya da Fati Shu'uma da Rashida Abdullahi da sauransu
Shugaba Buhari
Bayanan hoto, Ba wannan ne karon farko da shugaban ya fara shirya wa 'yan wasan Hausa liyafa ba
Shugaba Buhari
Bayanan hoto, Sai dai wadansu na danganta wannan liyafar da gabatowar babban zaben 2019
Shugaba Buhari
Bayanan hoto, A lokacin da yake yi musu jawabi, Shugaba Buhari ya ba su tabbacin ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa a kasar
Shugaba Buhari
Bayanan hoto, Cikin wadanda suka samu halartar taron har da mawaka kamarsu Ali Jita da Naziru M Ahmad da Fati Nijar da Dauda Kahutu wanda aka fi sani da Rarara da sauransu
Shugaba Buhari
Bayanan hoto, Har ila yau akwai jaruman fina-finai kamarsu Hamisu Iyantama da Adam A Zango da Nura Husseini da Rabi'u Rikadawa da
Shugaba Buhari
Bayanan hoto, Shugaba Buhari ya samu goyon bayan wadansu daga cikin 'yan Kannywood lokacin da ya lashe zaben 2015
Shugaba Buhari
Bayanan hoto, A karshe shugaban ya ce gwamnatin za ta ci gaba dakufa wajen yaki da matsalar satar fasaha wanda take ci wa masu shirya fina-finai a kasar tuwo a kwarya