Hotunan ziyarar da Buhari ya kai Bauchi

An wallafa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa jihar Bauchi domin jajantawa wadanda gobarar da aka yi a kasuwar garin Azare ta shafa da kuma bala'in guguwa a jihar.

Shugaban ya isa jihar da ke arewa maso gabashin kasar ne a ranar Alhamis da safe
Bayanan hoto, Shugaban ya isa jihar da ke arewa maso gabashin kasar ne a ranar Alhamis da safe.
A ranar Asabar ne aka yi wata mummunar guguwa a jihar wacce ta yi sanadin mutuwar mutum tare da jikkata wasu da dama, ta kuma lalata dukiyoyi.
Bayanan hoto, A ranar Asabar ne aka yi wata mummunar guguwa a jihar wacce ta yi sanadin mutuwar mutum tare da jikkata wasu da dama, ta kuma lalata dukiyoyi.
Bayan wannan iftila'i ne kuma wata mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwar da ke garin Azare na karamar hukumar Katagum a ranar Lahadi da daddare
Bayanan hoto, Bayan wannan iftila'i ne kuma wata mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwar da ke garin Azare na karamar hukumar Katagum a ranar Lahadi da daddare.
Shugaban ya fara kai ziyara fadar sarkin Katagum kafin ya kai ziyara kasuwar Azare
Bayanan hoto, Bayan da ya sauka a garin Bauchi, shugaban ya wuce garin Azare ne inda ya fara kai ziyara fadar Sarkin Katagum kafin ya kai ziyara kasuwar Azare.
Dubban magoya bayan shugaban ne suka yi masa maraba
Bayanan hoto, Dubban magoya bayan shugaban ne suka yi masa maraba.
Wani magoyin bayan shugaban rike da hotonsa cikin annashuwa
Bayanan hoto, Wani magoyin bayan shugaban rike da hotonsa cikin annashuwa.
Wadansu mata magoya bayan shugaban lokacin da suke kukan farin ciki bayan yin tozali da shugaban
Bayanan hoto, Wadansu mata magoya bayan shugaban lokacin da suke kukan farin ciki bayan yin tozali da shugaban.
An tsaurara tsaro a wuraren da shugaban ya ziyarta
Bayanan hoto, An tsaurara tsaro a wuraren da shugaban ya ziyarta.
Gobarar ta jawo asarar dumbin dukiya da kawo yanzu ba a tantance adadinta ba.
Bayanan hoto, Gobarar ta jawo asarar dumbin dukiya da kawo yanzu ba a tantance adadinta ba.
Jihar Bauchi na daga cikin jihohin da Shugaba Buhari ke da goyon baya sosai
Bayanan hoto, Jihar Bauchi na daga cikin jihohin da Shugaba Buhari ke da goyon baya sosai