Kalli hotunan bikin cika shekara 100 da kafa Kaduna

An wallafa

An gudanar da bikin Durbar cika shekara 100 da kafa garin Kaduna wanda ke arewacin Najeriya a ranar Asabar.

An gudanar da bikin Durba ne a dandalin Murtala Square a tsakiyar birnin, inda dubban jama'a suka halarta
Bayanan hoto, An gudanar da bikin Durba ne a dandalin Murtala Square a tsakiyar birnin, inda dubban jama'a suka halarta
A shekarar 1917 ne aka kafa garin Kaduna wanda yake yankin arewa maso yammacin Najeriya
Bayanan hoto, A shekarar 1917 ne aka kafa garin Kaduna wanda yake yankin arewa maso yammacin Najeriya
Manyan baki daga ciki da wajen jihar ne suka halarci bikin
Bayanan hoto, Manyan baki daga ciki da wajen jihar ne suka halarci bikin
Cikin wadanda suka halarci bikin har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Namadi Sambo
Bayanan hoto, Cikin wadanda suka halarci bikin har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Namadi Sambo
A shekarar 1917 ne aka kafa garin Kaduna wanda yake yankin arewa maso yammacin Najeriya
Bayanan hoto, Kek din bikin yayin wata liyafa da gwamnatin jihar ta shirya bayan kammala bikin Durban
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu yana daga cikin manyan sarakunan kasar da suka samu halartar bikin
Bayanan hoto, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu yana daga cikin manyan sarakunan kasar da suka samu halartar bikin
Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris shi ne yakasance mai masaukin baki yayin bikin
Bayanan hoto, Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris shi ya kasance mai masaukin baki yayin bikin
Durban
Bayanan hoto, An rika nishadantar da mahalarta bikin da kade-kade da bushe-bushe
Garin ya taba zama babban birnin jihar Arewa
Bayanan hoto, Garin ya taba zama babban birnin jihar Arewa
An yi kade-kade da raye-raye don nuna al'adun jama'a mabambanta na jihar Kaduna
Bayanan hoto, An yi kade-kade da raye-raye don nuna al'adun jama'a mabambanta na jihar Kaduna