An gano maganin sanƙo na har abada

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Tsirowar ƙananan ƙuraje a fatar jikin mutum na iya magance matsalar sanƙo watau rashin gashi a gaban goshi, kamar yadda wani bincike da aka wallafa a wannan makon a mujallar ya Nature ya bayyana.

Masana kimiyya a Jami'ar California da ke Irvine a Amurka sun kwashe kusan shekaru goma wajen bincike kan ƙurajen fata domin fahimtar dalilin da ya sa suke samar da dogon gashi. Sabon binciken ya nuna cewa irin waɗannan ƙuraje na ɗauke da wasu ƙwayoyin halitta na musamman waɗanda ke taimakawa wajen fiitowar gashi.

"Mun gano wani abu a gashin da ke tsirowa a saman waɗannan ƙuraje," in ji Maksim Plikus jagoran binciken kuma farfesa a fannin kimiyyar halittar ƙwayoyin jiki a Jami'ar California da ke Irvine.

Kowacce rana ɗan Adam kan rasa tsakanin gashi 50 zuwa 100, sannan jijiyoyin da ke samar da gashi su fidda wasu sabbi.

Sai dai ga mutanen da suka rasa gashi ko kuma suke fama da matsalar zubewar gashi wadda likitoci ke kira da suna alopecia ko androgenic alopecia, jijiyoyin da ke samar da gashin kan ne suke dai na aiki, lamarin da ke hana sabon gashi tsirowa.

A gwaje-gwajen da suka gudanar kan ɓeraye, Plikus da tawagarsa ta masu bincike sun nuna cewa wani sinadari mai suna osteopontin, wanda ake samu da yawa a cikin ƙurajen fata na iya zuƙo ƙwayoyin halittar da ke samar da gashi waɗanda a baya suka daina aiki.

Masu binciken sun yi gwaji ta hanyar shigar da wasu samfuran fatar jikin mutum cikin beraye sannan suka yi wa dabbobin allurar sinadarin har sau 3 tare da bayar da tazarar kwana guda tsakanin kowace allura.

Cikin ƴan kwanaki allurar ta taimakawa ɓerayen wajen fidda sabon gashi wanda tsawonsa ya kai santimita ɗaya.

Domin tabbatar da cewa sinadarin Osteopontin na fito da silin gashi, masu binciken sun yi allurar sinadarin Protein a wani ɓangaren fata da ba ya fidda gashi.

Plikus ya ƙara da cewa, saɓanin binciken da ya mayar da hankali akan gashin jikin beraye, sakamakon ya yi daidai da na ɗan Adam.

Plikus na fatan cewa bincikensa zai samar da maganin matsalar rashin gashi da zubewar gashi a nan gaba. Ya ce ana iya gudanar da irin wannan magani a asibitocin ƙwararrun likitocin fata kamar yadda ake gudanar da wasu hanyoyin gyaran jiki.

Ya kuma bayyana cewa kamar yadda ake sa rai mutanen da za a yi wa maganin za su sake samun gashi halitta mai kama da wanda suke da shi kafin fara zubewar gashin.

Akwai hanyoyi daban-daban na magance zubewar gashi da kuma sanƙo, amma ba dukkansu ne ingantattun hanyoyin magani da hukumomin lafiya suka amince da su ba. Hanyoyin sun haɗa da amfani da ƙwayoyin magani da kuma man da ake shafawa a fatar kai.

Wasu daga cikin waɗannan magunguna na iya haifar da matsaloli. Alal misali, maganin Rogaine na iya sa fatar jiki ta riƙa kaikayi ya yin da Propecia ke iya rage sha'awar jima'i da kuma kuzarin yin ta.

"Mun san hanyoyin da za mu bi don rage tasirin matsalar amma har yanzu ba mu da cikakken maganinta," in ji Dakta Jeremy Green, wani ƙwararren likitan fata a birnin Miami kuma mai ba da shawara a kamfanin Amplifica.

Sauran bincike

An gudanar da wasu bincike a baya waɗanda daga ciki akwai wani bincike da ya gano yiwuwar samar da maganin sanƙo ta hanyar amfani da wani magani da a baya ake amfani da shi wajen magance cututtukan ƙashi.

Masu binciken sun gano cewa wannan magani na iya toshe wani sinadari mai suna SFRP1, wanda ke hana bunƙasar gashi.

A lokacin jagoran binciken, Dakta Nathan Hawkshaw daga Jami'ar Manchester da ke Ingila, ya ce binciken na iya kawo sauyi a rayuwar mutanen da suka rasa gashinsu.

Wani mai magana da yawun Ƙungiyar Likitocin Fata ya shaidawa BBC cewa binciken na da muhimmanci kuma zai iya taimakawa wajen magance ƙarin buƙatar da ake samu ta neman hanyoyin magance matsalar zubewar gashi da sanƙo.

Ya ƙara da cewa ya kamata a gudanar da ƙarin bincike kafin a ba da shawarar amfani da wannan magani ga mutanen da ke fama da matsalar zubewar gashi.

Dashen gashi

Ya yin da ake ci gaba da fuskantar ƙarancin ingantattun hanyoyin magance sanƙo, a lokacin da mutane musamman maza ke fuskantar zubewar gashi fiye da kima, ana ci gaba da laluben wasu hanyoyin magance matsalar. Lamarin da ya sa dashen gashi ya ƙara samun karɓuwa cikin shekaru 10 da suka gabata.

A baya bayan nan, birnin Santanbul na ƙasar Turkiyya ya zama ɗaya daga cikin manyan wuraren da mutane daga sassa daban-daban na duniya ke zuwa domin dashen gashi musamman maza da mata masu fama da matsalar sanƙo.

Birnin na da cibiyoyin kiwon lafiya da ke gudanar da aikin dashen gashi ga mutanen da ke fama da matsalar sanƙo.

Ƴan Somaliya da dama na zuwa Turkiyya domin dashen gashi amma a baya-bayan nan an fara samun irin waɗannan ayyuka a yankin Gabashin Afirka.

An tabbatar da cewa biranen Mogadishu da Hargeysa da Addis Ababa da Nairobi duk sun samu fasahar dashen gashi.