'Wasu matan ba su san suna ɗauke da cutar da ke sa mace gemu ba'

Bayanan bidiyo, 'Wasu matan ba su san suna ɗauke da cutar da ke sa mace gemu ba'
'Wasu matan ba su san suna ɗauke da cutar da ke sa mace gemu ba'
An wallafa

Gemu ko gashin bakin da kuke gani a fuskar wasu mata, ba haka kawai ba ne. Larura ce!

An ware duk watan Satumba domin faɗakar da mutane cewa kimanin kashi 10% na mata suna da larurar rikicewar sinadaran jiki wato PCOS a taƙaice.

Albarkacin wannan wata, mun zanta da wata mai wayar da kai kuma da ke da wannan cuta domin jin suke fama.