Yadda aka baje kolin al'adun Najeriya a jami'ar Ahmadu Bello
Yadda aka baje kolin al'adun Najeriya a jami'ar Ahmadu Bello
An wallafa
Duk shekara shugabannin majalisar ɗalibai ta Jami'ar Ahmadu Bello na shirya taron baje-kolin al'adun al'ummar Najeriya.
ABU na daga cikin jami'o'in tarayya a Najeriya da suka fi tara ɗalibai daga jihohi da sassa daban-daban na ƙasar.
Bikin ya ƙunshi baje-kolin al'adun ƙabilu da al'umma daban-daban daga arewaci da kudancin ƙasar.
A shekarar 1962 ne aka kafa Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a matsayin jami'ar yankin arewacin Najeriya.



